Ganduje Ya Hadu da Shugaban Kasa, Tinubu Ya Magantu kan Zargin Kisan Kiristoci

Ganduje Ya Hadu da Shugaban Kasa, Tinubu Ya Magantu kan Zargin Kisan Kiristoci

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da masu yada jita-jitar cewa ana kisan kiyasin addini a Najeriya
  • Tinubu ya ce bayan shekaru 65 da samun ’yancin kai, ’yan Najeriya sun fahimci bambancin addini da al’ada
  • Shugaban ya kuma jaddada rawar APC cikin shekaru 10 da ta kwashe tana mulki, ya ce jam’iyyar ta kawo sauyi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Owerri, Imo – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi karin haske kan jita-jitar kisan Kiristoci a Najeriya.

Tinubu ya bayyana cewa babu wani kisan kiyashin addini da ake yi a Najeriya, ya ce duk irin jita-jitar da ake yadawa karya ce kawai don ta da hankali.

Tinubu ya kaddamar da aiki a Imo, Gnaduje ya halarta
Bola Tinubu yayin kaddamar da ayyuka a Imo da Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: Hope Uzodinma, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X bayan shugaban ya kai ziyara a jihar Imo.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu ya fada a jawabin ranar samun 'yanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya samu rakiyar yan siyasa zuwa Imo

Yayin ziyarar, Tinubu ya samu rakiyar jiga-jigan APC da sauran siyasa da suka raka shi zuwa jihar domin kaddamar da ayyuka.

Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, tsofaffin shugabannin APC biyu, Adams Oshiomhole da Abdullahi Umar Ganduje suna daga cikin mahalarta bikin.

Har ila yau, akwai gwamnonin jihohin APC, tare da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, wadanda suka halarci kaddamar da ayyukan da kuma ƙaddamar da littafi.

Kakakin Majalisar Wakilai, Mataimakinsa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, tsofaffin shugabannin majalisar dattawa da Sanatoci suma sun halarci bikin.

Tinubu ya ziyarci jihar Imo domin kaddamar da ayyuka
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Aiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Bola Tinubu ya shawarci yan Najeriya

Tinubu ya bayyana haka ne a Owerri, yayin kaddamar da littafin da Gwamna Hope Uzodimma ya rubuta a kan shekaru 10 na mulkin jam’iyyar APC.

Ya kuma yi amfani da taron wajen kaddamar da sababbin ayyukan more rayuwa da suka hada da titin Owerri-Mbaise-Umahia da gadojin sama.

Kara karanta wannan

'Tattali da tsaro,' Bangarori 23 da Tinubu ya tabo a jawabinsa na ranar 'yanci

Shugaban kasar ya ce Najeriya ta kai matakin da kowa ke fahimtar bambancin addini da al’ada a matsayin karfi, ba rauni ba, don haka babu wani addini da ke fusknar barazana.

Tinubu ya jaddada cewa bai kamata a bari wasu daga waje su raba ’yan kasa ba, ya ce Najeriya kasa ce mai girma, wacce take tafiya bisa amincewar ’yan ta.

Alkawarin Tinubu kan kare rayukan al'umma

A cewarsa, alhakin gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da cewa karfin bambancin al’umma ba zai zama rauni ba.

Game da rawar APC a mulkin kasar cikin shekaru 10, Tinubu ya ce jam’iyyar ta fitar da Najeriya daga rudani zuwa sabon tafarki.

Ya bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta fara shimfida tubalin da ya kai ga ingantaccen tsaro da ci gaban ayyukan more rayuwa.

Ya kara da cewa jam’iyyar APC ba cikakkiya ba ce, amma tana da tsari da hangen nesa, A cewarsa, gwamnati na kokarin gina kasa da ta dogara da aiki maimakon dogaro da tallafi.

Nigeria@65: Jawabin Tinubu ga 'yan Najeriya

Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tuna da jajircewar shugabannin farko na ƙasar da hangen nesansu na gina Najeriya.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a yau 1 ga Oktoba 2025

Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta tsallake yakin basasa, mulkin soja da rikice-rikicen siyasa kuma yanzu ta fara cigaba.

Bola Tinubu ya ce sauye sauyen gwamnati sun kawo ci gaba, inda tattalin arziki ya fara murmurewa kuma tsaro ke kara inganta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.