Nigeria @65: Jawabin da Tinubu Ya Yi wa 'Yan Najeriya a Yau 1 ga Oktoba 2025
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tuna da jajircewar shugabannin farko na ƙasar da hangen nesansu na gina Najeriya
- Ya bayyana cewa Najeriya ta tsallake yakin basasa, mulkin soja da rikice-rikicen siyasa kuma yanzu ta fara cigaba
- Bola Tinubu ya ce sauye sauyen gwamnati sun kawo ci gaba, inda tattali ya fara murmurewa kuma tsaro ke kara inganta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yau Najeriya ta cika shekara 65 da samun ’yancin kai tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce al’ummar ƙasar sun riga sun tsallake mawuyacin hali, inda ya ce matakan gwamnatinsa sun fara haifar da sauyi mai ma’ana.

Source: Facebook
Punch ta ce shugaban ya yi jawabi ne ranar ’yancin kai ta 2025 inda ya tuna da jajircewar shugabannin farko irin su Ahmadu Bello, Tafawa Balewa, Nnamdi Azikiwe da Obafemi Awolowo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya bayyana cewa duk da wahalhalu, ƙasar ta samu ci gaba sosai a fannoni da dama ciki har da ilimi, lafiya, sadarwa.
Kalubalen da Najeriya ta fuskanta
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa Najeriya ta fuskanci manyan ƙalubale, ciki har da yakin basasa, mulkin soja da rikice-rikicen siyasa.
Duk da haka, shugaban ya ce al’ummar kasar sun nuna jajircewa wajen kare martaba da ci gaban ƙasarsu.
A cewarsa, a lokacin samun ’yancin kai, Najeriya na da makarantun sakandare 120 da jami’a ɗaya, amma a yau adadin ya haura 23,000 tare da jami’o’i 274 da sauran cibiyoyin ilimi.
A kan haka shugaban kasar ya ce wannan misali ya nuna irin cigaban da aka samu cikin shekaru 65.
Maganar Tinubu kan tattalin Najeriya
Shugaban ya bayyana cewa ya gaji tattalin arziki mai rauni amma gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu wahala domin dawo da inganci.
Ya ce an kawo ƙarshen tallafin man fetur, an yi gyara kan darajar kudi, kuma hakan ya ba da damar amfani da kudin kasa a bangaren ilimi, lafiya, noma da sauran muhimman fannoni.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin jefa 'yan Najeriya miliyan 15 a bakin cikin talauci
A cewarsa, tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da 4.23% a 2025, mafi girma cikin shekaru huɗu, yayin da hauhawar farashi ya ragu zuwa 20.12%, mafi ƙanƙanta cikin shekaru uku.
Ya ƙara da cewa an samu cigaba a fannin kudin shiga daga bangaren man fetur da sauransu, inda ya ce asusun wajen Najeriya ya kai Dala biliyan 42.
Tinubu ya yi magana kan tsaron Najeriya
This Day ta wallafa cewa Tinubu ya ce dakarun tsaro na ƙasar suna samun gagarumar nasara kan ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma aikata ta’asa.
Ya bayyana cewa Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas da ’yan ta’addan IPOB a Kudu maso Gabas suna raguwa, yayin da al’ummomi da dama suka koma gidajensu.
Shugaban ya kara da cewa jami'an tsaro na cigaba da samun nasara a kan 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Arewa ta Yamma.

Source: Twitter
Shugaba Tinubu ya yi magana kan matasa
Shugaban ya bayyana matasa a matsayin babban jarin Najeriya, inda ya lissafo shirye-shiryen rance da tallafi da gwamnati ta ƙaddamar don inganta rayuwarsu.
Ya ce shirin NELFUND ya riga ya taimaka wa ɗalibai fiye da 500,000 da rancen kusan Naira biliyan 100.
Har ila yau, ya ce shirye-shirye irin su Credicorp, YouthCred da iDICE na bai wa matasa damar samun damar kudi, inganta fasaha domin yin tasiri a fannoni daban-daban.
Tinubu ya ce a rika biyan haraji
A ƙarshe, Tinubu ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen gina ƙasar da za ta zama abin alfahari.
Ya ce ana buƙatar kowa ya cigaba da biyan haraji, shiga noma domin samar da abinci, masana’antu da kuma tallafa kasa wajen sayen kayan da aka hada a Najeriya.
Legit ta tattauna da Amina Bulama
Wakilin Legit ya zaga jihar Gombe domin duba yadda bikin ranar 'yanci ya ke gudana a fadin jihar.
Ba kamar yadda ake a shekarun baya ba, wannar shekarar bikin bai yi armashi ba, duk da cewa wasu matasa sun taru a kofar gidan gwamnati suna daukar hoto domin murnar ranar.
Wata matashiya a jihar Yobe, Amina Bulama ta ce haka lamarin ya ke a jiharsu:
"Mutane suna fama da matsaloli da yawa. Ni kaina ban fita bikin ba, kuma mutane da yawa ba su je ba."
Ya kamata shugabannin su kara tausayawa domin hankalin mutane ya dawo kan lamarin kasa irin ranar 'yanci."
An soke faretin 1 ga Oktoban 2025
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta yi karin haske yayin da ake tsaka da batun bikin ranar 'yanci ta 2025.
A wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta fitar, ta sanar da soke faretin sojoji da aka tsara za a yi a karon farko.
Sai dai duk da haka, rahotanni sun bayyana cewa za a cigaba da sauran bukukuwan da aka tsara ba tare da wani sauyi ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


