Gwamna Abba Ya Kaddamar da Shirin Matasa, Kowane Zai Samu N150,000 a Kano

Gwamna Abba Ya Kaddamar da Shirin Matasa, Kowane Zai Samu N150,000 a Kano

  • Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin tallafawa matasa da kudin da za su kama sana'a ko bunkasa harkokin kasuwancin su a fadin jihar Kano
  • A rukunin farko na shirin da gwamna Abba Abba ya kaddamar yau Talata, kowane mutum daya daga cikin matasa 5,384 zai samu N150,000
  • Gwamna Abba ya bukaci wadanda ba su ga sunayensu a kashi na farko na shirin ba su yi hakuri, inda ya ce kashi na biyo zai fito nan kusa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin tallafawa matasa kashi na farko wanda gwamnatinsa ta shirya raba Naira miliyan 800 a fadin jihar Kano.

Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wannan shiri ne a wani bangare na yunkurin tallafawa matasan jihar Kano domin su dogara da kansu.

Kara karanta wannan

An shigar da 'yan sanda kotu, za a fara shari'a kan takaita hawa babur a Gombe

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf a wurin taro a jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya tallafawa matasa 5,384

Ya bayyana cewa an tsara shirin ne domin taimaka wa matasa ‘yan kasuwa wajen fara kasuwanci ko kuma faɗaɗa harkokin sana'o'insu.

A wurin bikin bikin ƙaddamarwar, Gwamnan ya bayyana cewa matasa maza da mata 5,384 ne za su amfana karkashin wannan shiri wanda shi ne kashi na farko.

Ya ce kowanne matashi daga cikin matasan zai samu tallafin ₦150,000, wanda a jimilla ya kai ₦800,700,000, a wani ɓangaren kudirin gwamnatinsa na inganta rayuwar matasa a jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir ya jaddada cewa an tsara shirin ne domin taimaka wa matasa su shiga harkar kasuwanci yadda ya kamata tare da bada gudummawa ga ci gaban al’umma.

Gwamnatin Kano za ta saki kashi na biyu

Ya roƙi waɗanda suka ci gajiyar shirin su yi amfani da kudin yadda ya dace don bunƙasa harkokinsu da kuma tabbatar musu da cewa hakan zai gina masu gobe mai kyau.

Kara karanta wannan

Da sauran rina a kaba: Gwamna Abba ya yi maganar cikar Najeriya shekara 65 da 'yanci

Haka kuma Gwamna Abba ya yi kira ga waɗanda ke cikin jerin wadanda ba su ga sunayensu a cikin kashin farko ba su yi haƙuri, tare da tabbatar musu cewa kashi na biyu na shirin zai fito nan ba da jimawa ba.

Abba ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa manufofi da shirye-shiryen da ke ƙarfafa matasa da samar da ingantaccen rayuwa a fadin jihar Kano fifiko.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Abba ya ja hankalin mukarrabansa

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci duka hadimansa da masu rike da mukaman siyasa su kasance masu gaskiya da rikon amana.

Gwamna Abba ya bukaci masu rike da mukaman siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati da su yi duk mai yiwuwa su tabbata sun sauke nauyin da aka dora masu.

Da yake gargadi kan cin hanci, Abba ya jaddada cewa rashawa na cutar da talakawa da marasa galihu, yana mai cewa mutanen Kano sun fara gajiya da alkawurran da ba a cikawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262