An Yi Kwanton Bauna an Harbe Dan Bindigan da Ya Tuba bayan Fara Shiga Jama'a

An Yi Kwanton Bauna an Harbe Dan Bindigan da Ya Tuba bayan Fara Shiga Jama'a

  • An kama mutum daya bisa zargin hannu a kisan wani tsohon dan bindiga a yankin Zaki-Biam, jihar Benue
  • Rahotanni sun ce tsohon dan bindigan ya rasa ransa ne bayan wasu mutane sun bi shi a babur sun harbe shi
  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa tana cigaba da bincike domin kama sauran wadanda suka gudu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta tabbatar da cafke wani mutum da ake zargi da hannu a kisan wani tsohon dan ta’adda.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a yankin Sankera Zaki-Biam, karamar hukumar Ukum.

Taswirar jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiya
Taswirar jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiya. Hoto: Legit
Source: Original

Legit Hausa ta samu bayanai kan yadda aka kashe tsohon dan bindigar ne a wani ako da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

An lakadawa dan damfara duka bayan asirin shi ya tonu a tsakiyar kasuwar Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka kashe tsohon dan bindigan?

Lamarin ya faru ne a ranar 29 ga Satumba, inda aka ce wasu da bindigogi dauke da babur suka bi tsohon dan ta’addan suka harbe shi har lahira.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ya tabbatar da cewa an dauki gawar wanda aka kashe an kuma mika ta dakin ajiye gawawwaki na babban asibitin Zaki-Biam.

Waye tsohon dan bindigan da ya mutu?

An bayyana sunan tsohon dan bindigan da Kyoga Joka, da aka ce ya mika wuya ga hukuma bayan tuba.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun bishi ne har suka hallaka shi a bainar jama’a, lamarin da ya girgiza mazauna yankin.

Wani ganau ya ce wadanda suka harbe Joka sun gudu ta hanyar wani daji bayan kisan, inda suka bar jama’a cikin firgici da tsoro.

Waye ake zargi da kisan Joka?

A cewar shaidun gani da ido, wadanda suka aikata harin suna cikin mabiyan wani babban dan ta’adda da ake kira Chen.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya, ciki har da kwamishina a Neja

An ce suna karkashin kungiya ce da ta dade tana addabar yankin Sankera da hare-hare, kashe-kashe da satar jama’a.

Hakan ya kara tabbatar da damuwar jama’a kan yadda kungiyoyin ta’addanci ke ci gaba da yi wa al’umma barazana duk da ikirarin samun sauki daga bangaren wasu da suka tuba.

Gwamna Alia yana yi wa manema labarai bayani
Gwamna Alia yana yi wa manema labarai bayani. Hoto: @HyacinthAlia
Source: Facebook

An kama mutum 1 da ake zargi

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta samu nasarar cafke wani mutum mai suna Teryila Kpogh wanda ake zargin mamba ne na kungiyar Chen, ana zargin shi da hannu a kai tsaye wajen kashe Joka.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa tuni aka mika batun zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na SCID domin gudanar da bincike mai zurfi.

Rundunar ta ce tana cigaba da kokarin kamo sauran wadanda suka gudu daga cikin wadanda ake zargi.

An kama dan damfara a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Neja ta sanar da kama wasu mutane da ake zargi da aikata laifuffuka.

Rahoto ya nuna cewa daga cikin mutanen da aka tabbatar da kama wa akwai wanda ake zargi ya yi fice a damfara.

Kara karanta wannan

An shigar da 'yan sanda kotu, za a fara shari'a kan takaita hawa babur a Gombe

An kama dan damfarar da ake zargi ne bayan ya je wani shago da jaka cike da takardu yana ikirarin cewa kudi ne.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng