Rubutu kan Tinubu Ya Jawo an Maka Tsohon 'Dan Takarar Shugaban Kasa a Kotun Abuja
- Gwamnatin Tarayya ta kai karar fitaccen dan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore gaban babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja
- Ana zargin Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya da amfani da shafinsa na X wajen cin mutuncin Shugaba Bola Tinubu
- Sai dai bayan kiran karar, wadanda ake tuhuma sun zargi gwamnatin tarayya da kin tura masu takardar tuhuma kamar yadda doka ta tanada
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya kai karar ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore, bisa tuhume-tuhume biyar da suka shafi wallafa sakon karya da cin mutuncin Shugaba Bola Tinubu a shafin sada zumunta.
Kamfanin X (wanda a da ake kira Twitter) da Meta (kamfanin Facebook, Whatsapp da Instagram) na cikin waɗanda ake tuhuma a shari'ar Sowore a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan
'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane

Source: Twitter
Wane rubutu ya sa aka maka Sowore a kotu?
Jaridar Leadership ta tattaro cewa masu gabatar da kara sun zargi Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa da amfani da shafinsa na X wajen wallafa wannan sako:
"Wannan mai laifin @officialABAT ya tafi Brazil yana cewa babu cin hanci a gwamnatinsa. Wace irin ƙarfin guiwa ne ya sa shi yin wannan ƙarya ba tare da jin kunya ba?”
Masu kara sun ce wannan sakon da ya wallafa a ranar 25 ga Agusta, 2025 ya saba wa Sashe na 24(2)(b) na Dokar Hana Laifuffukan Intanet ta 2024.
A cewarsu, dokar ta hana amfani da na’urar kwamfuta wajen yada bayanan ƙarya da ka iya haddasa rikici wanda zai zama barazana ga tsaro da karya doka.
Lauyoyin gwamnati sun dage cewa wannan magana an yi ta ne da nufin tayar da hankalin jama’a da kuma haifar da ƙiyayya ga Shugaban ƙasa.
Yadda zaman farko ya gudana a Abuja
Lokacin da aka kira shari’ar, Sowore ta bakin babban lauyansa, Abubakar Marshall (Esq.), ya yi ƙorafin cewa bai ga kwafin takardar tuhuma ba kamar yadda doka ta tanada.
Haka kuma, ya ce wanda ake tuhuma na biyu, wato X, shi ma bai samu kwafin takardar ba, kuma tunda shari’ar ta haɗin gwiwa ce, ba zai yiwu a ci gaba ba.
Babban lauya a Najeriya, Farfesa Tayo Oyetibo (SAN) shi ne ya wakilci kamfanin Meta, wanda ake tuhuma na uku, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Source: Twitter
Da yake martani, lauyan gwamnatin tarayya kuma Daraktan Gabatar da Ƙarar Jama’a (DPPF), Mohammed Babadoko Abubakar, ya ƙaryata zargin, yana mai cewa an tura takardar karar ga Sowore.
Alkalin kotun, Mai Shari'a Mohammed Garba Umar, ya dage shari’ar zuwa 27 ga watan Oktoba, 2025 bayan gano cewa gwamnati ba ta mika takardar tuhuma ga Sowore ba.
Sowore ya kai korafin Wike a Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa dan gwagwarmaya, Sowore ya shigar da ƙorafi a gaban Babban Lauyan jihar Florida da ke Amurka kan Nyesom Wike.
A cikin zungureriyar takardar korafin, Sowore ya nemi a kwace kadarorin da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya mallaka a ƙasar Amurka.
Omoyele Sowore ya zargi Wike da sayen gidaje uku a Winter Springs da ke jihar Florida da darajarsu ta kai Dala miliyan shida duk da kuɗin 'haram'.
Asali: Legit.ng

