Dangote: 'Yan Kwadago Sun Hade Kai, NLC na Shirin Taya PENGASSAN a Rufe Najeriya

Dangote: 'Yan Kwadago Sun Hade Kai, NLC na Shirin Taya PENGASSAN a Rufe Najeriya

  • Kungiyar kwadago ta kasa, NLC ta bayyana takaicin yadda matatar Dangote ta raba mutane 800 da aiki saboda shiga kungiya
  • Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero ya ce wannan mataki da matatar ta dauka ya saba da ka'idojin aiki a Najeriya da Duniya
  • Ya umarci dukkanin kungiyoyin da ke karkashin NLC da su zauna a cikin shirin tsunduma gagarumin yajin aiki a nan kusa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta umarci dukkannin ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da su fara shirye-shiryen yajin aikin ƙasa baki ɗaya.

Wannan ya biyo bayan daga da kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta kasa PENGASSAN ta yi da matatar Dangote a kan korar ma'aikata da wasu bukatu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga rikicin Dangote da PENGASSAN, ya fadi abin kunyar da zai faru ga Najeriya

NLC sun caccaki Matatr Dangote
Hoton Joe Ajaero da wasu ma'aikatan Najeriya Hoto: Nigeri Labour Congress HQ
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa wannan umarni na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban NLC, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta bi bayan PENGASSAN, ta soki Dangote

Premium Times ta wallafa cewa NLC ta zargi matatar Dangote da take dokokin ƙwadago na Najeriya, kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar ƙasashen duniya (ILO).

Ta ce korar ma’aikata sama da 800 bisa zargin shiga ƙungiyar ƙwadago haramun ne, kuma ya saba da ka'idojin daukar aiki a duniya baki daya.

Ajaero ya bayyana matatar Dangote a matsayin wurin danniya, inda ake tauye mutuncin ma’aikata domin samun riba mai yawa.

Kungiyar NLC ta zargi Dangote da danniya

Shugaban NLC, Joe Ajaero ya kara da cewa lamarin da ke faruwa a matatar Dangote ba karamin rikici ba ne.

Ya kara da cewa abin da ake gani yanzu, alama ce ta danniya a tsarin masana’antu a karkashin ra’ayin jari hujja da ke kokarin hana ma’aikata shiga ƙungiyoyi da tauye musu ‘yanci.

Kara karanta wannan

Rikicin Dangote da PENGASSAN: Ndume ya bukaci Tinubu ya ɗauki mataki mai tsauri

NLC ta zargi Dangote da karya doka
Hoton daya daga cikin motocin kamfanin Dangote, da Aliko Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

A cewarsa:

“Kowane reshe na ƙungiya ya kafa kwamitin shirin da yajin aiki kuma ya tuntubi ofishin NLC a cikin awanni 72.”

Ya ce ya zuwa yanzu an shiga matakin gaggawa inda kowane reshen ƙungiya ya kamata ya fara kamfen na ƙarfafa shigar ma’aikatan Dangote cikin ƙungiyar ƙwadago a duk inda suke aiki.

Sai dai gwamnatin tarayya ta nemi sasanci domin kaucewa tabarbarewar al’amura, inda ta yi kokarin zama da hukumomin matatar Dangote da kungiyar PENGASSAN.

An gaza sulhu tsakanin PENGASSAN da Dangote

A baya, kun samu labarin cewa kungiyar manyan ma’aikatan iskar gas da man fetur ta kasa (PENGASSAN) ta bayyana cewa tana nan daram akan matsayinta na ci gaba da yajin aiki.

Matsayar kungiyar na zuwa duk da kokarin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi na kokarin sasanta sabanin da ya kunno kai a tsakanin matatar Dangote da PENGASSAN.

Yajin aikin ya samo asali ne daga korar ma’aikata fiye da 800 da matatar Dangote ta yi, lamarin da ƙungiyar PENGASSAN ke kallon keta hakin ma’aikata ne da karya yarjejeniyar kwadago.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng