An Lakadawa Dan Damfara Duka bayan Asirin Shi Ya Tonu a tsakiyar Kasuwar Neja

An Lakadawa Dan Damfara Duka bayan Asirin Shi Ya Tonu a tsakiyar Kasuwar Neja

  • Rundunar y‘an sanda ta sanar da cafke mutum uku a jihar Neja da ake zargi da zamba, fashi da makami da kuma ta’addanci
  • Wani mutum daga Jihar Kebbi ya shiga hannun hukuma bayan ya yi yunkurin damfarar kudi sama da N500,000 a Kontagora
  • Wani artabu ya barke a kasuwa lokacin da jama’a suka yi yunkurin kashe dan damfarar, amma ‘yan sanda suka kubutar da shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja - Rundunar ‘yan sanda a jihar Neja ta sanar da cafke wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban ciki har da fashi da makami da kuma zamba.

Hakan ya biyo bayan sintiri da kuma samamen da rundunar ta gudanar a sassan jihar domin murkushe miyagun ayyuka.

Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode. Hoto: NIgeria Police Force
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa daga cikin wadanda aka kama har da wani matashi daga jihar Kebbi wanda ya shiga hannun ‘yan sanda bayan ya yi yunkurin damfara a kasuwar Kontagora.

Kara karanta wannan

An shigar da 'yan sanda kotu, za a fara shari'a kan takaita hawa babur a Gombe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun yi samame a Minna

A ranar 25 ga Satumba da misalin karfe biyu na dare, rundunar ta tura jami’an sashen yaki da ta’addanci zuwa yankin Sabon-Titi a Tunga, Minna.

A nan ne aka kama wasu matasa biyu, Murtala Abbas mai shekara 18 daga Katsina da Hassan Ibrahim mai shekara 20 daga Sabon-Titi.

An kama Abbas dauke da adduna biyu masu kaifi da ake zargin ana amfani da su wajen kai farmaki.

Haka kuma, an kama Ibrahim da bindigu guda biyu na gida, rigar ‘yan sanda, kayan maye da sauransu a tattare da shi.

An kama dan damfara a Neja

A wani samame dabam, jami’an 'yan sanda a Kontagora sun kama wani mai suna Bashir Abubakar dan asalin jihar Kebbi.

An ce ya shiga wani shago a kasuwar New Market da niyyar sayen waya da wasu abubuwa da darajarsu ta kai N500,000.

Kara karanta wannan

An kama bindigogi AK 47 a Kano, masu laifi 105 sun shiga hannun 'yan sanda a Satumba

Ya bar jaka ga mai shagon yana zargin zai dawo ya biya kudin, sai dai daga baya aka gano jaka cike take da takardu.

An ce an tabbatar da cewa ya yi yunkurin yin irin wannan zamba a watan Agusta inda ya kwashe wayoyi da darajarsu ta kai N240,000 ya tsere.

Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

An ladakadawa dan damfara duka

Lokacin da aka gano wannan mummunan aiki, jama’a sun fusata suka nemi kashe shi bayan lakada masa duka.

Sai dai jami’an ‘yan sanda sun isa wurin da gaggawa suka kwace shi daga hannun mutanen kafin su halaka shi.

Kakakin rundunar ya tabbatar da cewa yanzu haka an tsare da shi, kuma za a kammala bincike a shigar da shi kotu domin fuskantar hukunci.

An kama makamai a jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana nasarorin da ta samu a watan Satumban 2025.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan sandan jihar sun kama bindigogi kirar AK-47 da wasu kiran gida a jihar.

Kakakin 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun kama miyagun kwayoyi da suka kai kusan darajar Naira miliyan 100.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng