An Shigar da 'Yan Sanda Kotu, za a Fara Shari'a kan Takaita Hawa Babur a Gombe

An Shigar da 'Yan Sanda Kotu, za a Fara Shari'a kan Takaita Hawa Babur a Gombe

  • Wani lauya ya kai karar rundunar ‘yan sandan jihar Gombe saboda hana hawa babura a birnin Gombe na wasu lokuta
  • Lauyan mai suna Usamatu Abubakar ya ce wannan doka ta saba wa kundin tsarin mulki da hakkin dan Adam
  • Rahotanni sun nuna cewa kotu za ta fara sauraron karar a ranar Talata, 30 ga Satumba, 2025 da misalin karfe 9:00 na safe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Wani lauya mai suna Usamatu Abubakar ya kai kara gaban babbar kotun tarayya bisa zargin tauye hakkin jama’a da rundunar ‘yan sanda ta jihar ta aikata.

Wannan ya biyo bayan hana hawa babura da aka kafa daga karfe 7:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe a jihar Gombe.

Kwamishinan 'yan sandan Gombe, lauyan da ya shigar da kara da gwamnan jihar
Kwamishinan 'yan sandan Gombe, lauyan da ya shigar da kara da gwamnan jihar. Hoto: Buhari Abdullahi|Usamatu Abubakar|Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan shari'ar da za a yi ne a cikin wani sako da Usamatu Abubakar ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

An yi kwanton bauna an harbe dan bindigan da ya tuba bayan fara shiga jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka saka dokar a Gombe?

Legit Hausa ta rahoto cewa tun a watan Yulin 2025 rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta ayyana dokar.

Dokar ta jawo ce-ce-ku-ce tun bayan kafa ta a watan Yuli, inda jama’a da dama suka nuna rashin jin dadinsu.

A cewar masu suka, matakin ya jefa masu dogaro da babura cikin halin kunci, musamman masu sana’ar sufuri da masu amfani da su wajen harkokin yau da kullum.

Dalilin shiga kotu kan dokar babur

Usamatu Abubakar ya bayyana cewa hana hawa babura daga dare zuwa safe ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Lauyan ya bayyana cewa za a fahimci haka ne a karkashin babi na 4 wanda ya tanadi kariya ga hakkin dan Adam.

Ya kara da cewa, rundunar ‘yan sanda ba ta da hurumin kafa irin wannan doka ba tare da bin tsarin doka da ka’ida ba.

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya. Hoto: Ismaila Uba Masilli
Source: UGC

Saboda haka, ya ce daukar matakin zuwa kotu shi ne hanya mafi dacewa domin tabbatar da adalci ga al’umma.

Kara karanta wannan

An lakadawa dan damfara duka bayan asirin shi ya tonu a tsakiyar kasuwar Neja

Sanarwar kotu kan karar da aka shigar

Takardar sanarwar kotu da Legit Hausa ta samu ta nuna cewa za a fara sauraron shari’ar ne a kotun tarayya.

Rahotanni sun nuna cewa an tsara za a fara shari'ar ne da misalin karfe 9:00 na safe a ranar 30 ga Satumba, 2025.

Kotun ta umarci bangarorin biyu da su kasance a shirye da hujjoji da shaidu domin kare matsayinsu.

Wannan mataki yana nufin fara bin diddigi kan ko dokar ta yi daidai da kundin tsarin mulki ko akasin haka.

Lauya ya nemi goyon bayan jama'a

A cikin jawabin sa, Usamatu Abubakar ya roki jama’a da su mara masa baya da addu’a, yana mai fatan kotu za ta yi adalci a wannan shari’a.

Ya ce dokar ta shafi jama’ar jihar gaba daya wadanda aka tauye musu hakkin su na walwala da yin amfani da hanyoyin sufuri.

Legit ta tattauna da Usamatu Abubakar

Bayan zaman kotu na farko, Legit Hausa ta tattauna da lauyan da ya shigar da kara domin jin halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

"Sai an je gaban kotu," Fadar shugaban kasa ta kara tabo batun takarar Jonathan a 2027

Lauyan ya ce:

"An yi zaman farko a yau. Amma an dage shari'ar zuwa ranar 8 ga Okotoba, 2025,"

'Yan bindiga sun yi kisa a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wani mutum a jihar Gombe.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace mutumin ne a karamar hukumar Dukku, kuma an kashe shi bayan biyan kudin fansa.

Baya ga sace mutumin, wadanda ake zargin sun sace wasu mutane biyu a Dukku tare da wata matar aure duk a yanki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng