Gwamna Ya Shiga Rikicin Dangote da PENGASSAN, Ya Fadi Abin Kunyar da Zai Faru da Najeriya

Gwamna Ya Shiga Rikicin Dangote da PENGASSAN, Ya Fadi Abin Kunyar da Zai Faru da Najeriya

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna takaicinsa kan takaddamar da ke faruwa tsakanin matatar Dangote da kungiyar PENGASSAN
  • Abdullahi Sule ya nuna cewa idan abubuwa suka kai ga durkushewar matatar, lallai Najeriya za ta sha kunya a idon duniya
  • Gwamnan ya bukaci bangarorin da su hau kan teburin tattaunawa domin warware dukkanin matsalolin da ake takaddama a kansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan takaddamar kungiyar PENGASSAN da matatar Dangote.

Gwamna Sule ya ce Najeriya za ta fuskanci tozarci a idon duniya idan rikice-rikice suka dakile harkokin matatar man Dangote.

Gwamna Sule ya yi magana kan rikicin Dangote da PENGASSAN
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, na jawabi a wajen wani taro Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Politics Today na Channels Tv a ranar Litinin, 29 ga watan Satumban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sule ya ce kan rikicin PENGASSAN-Dangote

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya gayawa gwamnonin Arewa gaskiya kan rashin tsaro

Ya bayyana matatar a matsayin “kadarar kasa,” tare da yin kiran shiga tattaunawa tsakanin shugabannin matatar, kungiyoyin ma’aikata da kuma gwamnati.

Gwamnan ya ce matatar ta ceci Najeriya daga nauyin biyan kuɗin shigo da man fetur masu yawa da kuma kalubalen da ke tattare da samar da fetur.

"Abin da ya faru shi ne akwai gibi a fannin sadarwa, PENGASSAN, a yau, ya kamata ta zauna da Dangote."
“Ba za mu iya jure yanayin da za a rushe irin wannan cibiyar ba, a gaskiya, duniya za ta yi mana dariya."
"Matatar Dangote ba ta Dangote kaɗai bace. Ta Najeriya ce. Ta ceci Najeriya daga matsaloli da yawa. Yanzu Najeriya ba za ta damu da matsalar taki da sinadarai ba."
"Ina rokon PENGASSAN, shugabannin Dangote da gwamnatin tarayya su tabbatar an warware batun."
"Matatar Dangote ta zo dawwama ne, har ma tana fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje. Ba za mu iya jure matsaloli kan wannan cibiya ba."

- Gwamna Abdullahi Sule

Gwamna Sule ya kare matatar Dangote

Kan zarge-zargen korar ma’aikata da yawa, gwamnan ya kare matsayar matatar, yana mai cewa dakatar da isar iskar gas zai iya rushe ayyukanta.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gwangwaje magidanta da tallafi bayan tsuntsaye da kwari sun tafka barna

"Dangote bai tashi haka kawai ya kori dukkan ma’aikatan da ake zargi ba, yana bukatar mutane da za su gudanar da matatarsa. Yana da dubban ma’aikata."

- Gwamna Abdullahi Sule

Gwamna Sule ya kare matatar Dangote kan korar ma'aikata
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Karanta wasu labaran kan takaddamar Dangote da PENGASSAN

Gwamna Sule ya ba gwamnonin Arewa shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ba da shawara ga gwamnonin Arewa kan matsalar rashin tsaro.

Gwamna Sule ya bayyana cewa ya kamata gwamnonin su tashi tsaye wajen magance matsalar rashin tsaro, sannan su daina dora alhakin matsalar a kan waau

Ya bayyanaa yanzu gwamnatocin jihohi suna da isassun kudin da za su iya aiwatar da abubuwa da dama, saboda abin da suke samu daga asusun tarayya ya ninka har sau hudu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng