Batanci: Malaman Izala Sun Yi Zama kan Maganar 'Sakin' Abduljabbar Nasiru Kabara
- Kungiyar Ahlussunnah Wal-Jama’ah ta Kano ta yi taron manema labarai kan kalaman mataimakin gwamnan Kano da suka ce sun saba da gaskiya
- Kungiyar ta bayyana cewa shari’ar Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara ta gudana ne bisa gaskiya da hujjoji ba tare da siyasa ta shiga ba
- Ta bukaci gwamnatin Kano ta bayyana matsayinta a fili idan har tana da niyyar sako Abduljabbar Kabara daga gidan gyaran hali bayan tsare shi da aka yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Kungiyar Ahlussunnah Wal-Jama’ah a jihar Kano ta gudanar da taron manema labarai a Kano a ranar Litinin, 29, Satumba, 2025.
Ta yi taron ne domin mayar da martani kan kalaman mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Source: Facebook
A wani bidiyo da Freedom Radio ya wallafa a Facebook, kungiyar ta ce mataimakin gwamnan ya yi furuci ne a wajen Mauludi a masallacin Turasul Islam, Gwauron Dutse.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bidiyon, an ji Sheikh Muhammad Muslim Ibrahim wanda Farfesa ne a jami'ar Al-Qalam a Katsina yana gabatar da jawabi.
Kungiyar ta ce ya yi nuni da cewa shari’ar da aka yi wa Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara na iya kasancewa mai alaka da siyasa.
Wannan magana ta jawo ce-ce-ku-ce, abin da ya sa kungiyar ta kira taron domin fayyace matsayinta da kuma kare sahihancin shari’ar.
Zargin da aka yi wa mataimakin gwamna
Kungiyar ta bayyana cewa kalaman mataimakin gwamnan suna da hatsari domin suna iya rage darajar kokarin malamai da kotun Shari’a wajen kare martabar Annabi Muhammadu (SAW).
Haka zalika, sun ce kalaman na iya jefa al’ummar Kano cikin rudani, inda za su yi tunanin gwamnati na da wata boyayyar manufa.
Sun kuma bayyana cewa irin wadannan kalamai na iya zama hujja ga masu neman a saki Abduljabbar ko kuma wadanda ke son jefa wasu malaman cikin irin wannan matsala.
Karin haske daga kungiyar malamai
Kungiyar Ahlussunnah ta ce Abduljabbar ya yi kalaman da suka sabawa Annabi Muhammadu (SAW) a fili, sannan aka ba shi damar kare kansa a gaban malamai da kotu.
Awaisu Al'Arabee Fagge ya wallafa bidiyo a Facebook, inda kungiyar ta ce kotun Shari’a ta ba shi lauya, ta kuma saurari shaidu da bayanansa, kafin ta yanke hukunci cikin gaskiya.
Saboda haka, kungiyar ta tabbatar cewa shari’ar da kotu ta gudanar ba ta da alaka da siyasa, illa bin adalci da ka’ida.
Matsayin kungiyar malaman Kano
Kungiyar ta ce ba za ta lamunci duk wani yunkurin da zai mayar da batun da ya shafi Annabi (SAW) da addini cikin siyasa ba.
Ta bukaci gwamnatin Kano ta fito fili ta bayyana matsayinta, musamman idan har akwai shirin sake duba hukuncin da aka yanke wa Abduljabbar.
Sun bayyana cewa bai kamata gwamnati ta bari kalaman shugabanni su zubar da martabar shari’a da kuma ruguza zaman lafiya a jihar ba.

Source: Facebook
Taron ya gudana karkashin jagorancin Farfesa Muhammad Muslim Ibrahim, wanda ya rattaba hannu a madadin kungiyar Ahlussunnah Wal-Jama’ah ta Kano.
Kiran Sheikh Khalil ga malaman Kano
A wani rahoton, kun ji cewa, shugaban malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya yi kira ga malamai kan sabanin da ake samu.
Malamin ya bayyana cewa zaman mukabala da ake yi a jihar ba zai taba kawo maslaha kan sabanin da ake samu ba.
Ya bukaci malamai da gwamnati su dauki matakin zama da fahimtar juna wajen saka ka'idojin wa'azi maimakon mukabala.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


