Yajin Aiki: ASUU Ta Sake Yin Barazana ga Gwamnatin Tarayya
- Akwai yiwuwar a samu tsaikon karatu a jami'o'in Najeriya biyon bayan sabon wa'adin da kungiyar ASUU ta ba gwamnatin tarayya
- Kungiyar ASUU ta yi barazanar cewa za ta tsunduma yajin aiki idan har gwamnatin Najeriya ba biya mata bukatunta ba
- Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Chris Piwuna ya koka kan yadda gwamnati ta yi biris da bukatun da suka dade suna nema
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta yi barazanar tsunduma yajin aiki.
Kungiyar ASUU ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14, tana barazanar shiga yajin aiki idan har ba a biya mata bukatunta ba.

Source: Getty Images
Jaridar TheCable ta ce shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar bayan taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da aka gudanar a Jami’ar Abuja ranar Lahadi.

Kara karanta wannan
Tajudeen: Shugaban majalisa ya hango lokacin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya
Kungiyar ASUU ta soki gwamnatin tarayya
Farfesa Chris Piwuna ya soki abin da ya kira kunnen uwar shegun da gwamnatin tarayya take yi wajen cika musu bukatunsu, rahoton Tribune ya tabbatar da labarin.
ASUU ta bayyana cewa idan gwamnatin tarayya ta gaza magance matsalolin cikin wa’adin makonni biyu, za ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu, sannan ta shiga yajin aikin gama-gari kuma na dindindin.
Kungiyar ta koka kan durkushewar harkar ilimin jami’a da kuma muguwar dabi’ar gwamnati ta raina makarantun gwamnati.
Ta tunatar da cewa wannan barazanar ta biyo bayan zanga-zangar lumana da ta gudanar a jami’o’in tarayya da na jihohi a watan Agusta, wadda bata haifar da sakamako mai kyau ba.
"Yanzu shekaru fiye da 16 kenan da ASUU take gabatar da waɗannan matsaloli a gaban ‘yan jarida da al’umma."
“ASUU na da tabbacin cewa shugabannin Najeriya na da ikon gyara jami’o’in kasar nan."
- Farfesa Chris Piwuna
Wadanne bukatu ASUU ta lissafo?
Kungiyar ta jero batutuwa bakwai da aka daɗe ana muhawara a kansu sama da watanni uku.

Source: Twitter
Bukatun sun hada da:
- Sabunta yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta 2009.
- Samar da kuɗi don farfaɗo da jami’o’i.
- Magance matsalar cin zarafin malamai a wasu jami’o’in tarayya.
- Biyan bashin kaso 25–35% na karin albashi da aka biyo.
- Warware batun matsalolin karin girma da suka makale sama da shekaru huɗu.
- Warware matsalolin cire kuɗi a albashi
"ASUU ta yi amanna cewa gwamnati na da karfin da za ta iya hana wannan yajin aiki da ke gabatowa."
- Farfesa Chris Piwuna
Batun yajin aikin SSANU da NASU
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyoyin ma'aikatan manyan makarantu da ba malamai ba (NASU) da na ma'aikatan manyan makarantu (SSANU), sun yi maganar shiga yajin aiki.
Kungiyoyin sun koka kan yadda gwamnatin tarayya ta gaza cika musu alkawuran da ta daukar musu, da yin biris da bukatunsu.
Manyan kungiyoyin sun ba gwamnati karin wa’adi wanda zai bai wa gwamnati damar shawo kan matsalolin kafin su dauki matakin shiga yajin aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

