Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban Hukumar PSC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Tsohon Shugaban Hukumar PSC, DIG Perry Osayande, ya rasu yana da shekaru 88 ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025
- Hukumar PSC ta tabbatar da rasuwar Oasayande a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Ikechukwu Ani, ya rattaba wa hannu
- Marigayin dai ya ba da gudummuwa matuka a lokacin da yake aikin dan sanda da kuma lokacin da ya shugabanci hukumar PSC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon shugaban Hukumar Jin Dadin 'Yan Sanda ta Najeriya (PSC), Perry Osayande, ya riga mu gidan gaskiya.
Osayande, wanda ya kai matsayin mataimakin Sufeta Janar na kasa (DIG) kafin ya yi ritaya, ya rasu a ranar Lahadi a garin Benin, babban birnin jihar Edo.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta tattaro cewa tsohon DIG na rundunar yan sandan ya bar duniya yana da shekaru 88 da haihuwa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ya ya fitar a jiya Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025.
Gudummuwar da Osayande ya bayar a PSC
Ani ya bayyana Osayande a matsayin “kwararren ɗan sanda mai ilimi da hangen nesa, wanda ya taka rawar gani a aikinsa kuma ya jagoranci hukumar cikin kwarewa.”
“DIG Osayande shi ne ya gaji Cif Simon Okeke, wanda shi ne shugaban farko na hukumar jin dadin yan sanda. An naɗa Osayande a watan Afrilu 2008 lokacin mulkin Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.
“A lokacinsa, ya kawo ci gaba matuka ciki har da amincewar shugaban ƙasa wajen gina babbar hedkwatar hukumar PSC da yanzu take a unguwar Jabi a Abuja.
"Marigayi DIG Parry Osayande mutum ne jarumi, mai hazaka da kwarin gwiwa, wanda hakan ya taimaka wajen ɗora hukumar a turba mai kyau tun a farkon kafuwarta.”
- Ikechukwu Ani.
Hukumar PSC ta roki addu'a daga yan Najeriya
Shugaban PSC na yanzu, DIG Hashimu Argungu (mai ritaya), ya bayyana mutuwar DIG Osayande a matsayin babban rashi ga hukumar.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su sanya hukumar PSC a addu’o'insu, musamman ganin cewa hukumar ta rasa tsofaffin shugabanninta biyu cikin wata guda.
Takaitaccen bayani kan DIG Perry Osayande
An haifi Osayande a Benin a shekarar 1936. Ya shiga aikin ’yan sanda a 1960, sannan ya yi ritaya a matsayin mataimakin Sufeto Janar na ’yan sanda (DIG) a 1992.
Ya yi aiki a matsayin kwamishinan ’yan sanda a tsohuwar jihar Bendel, ya shiga cikin ayyukan da suka dakile tarzoma a Bauchi da Kano a farkon shekarun 1990.

Source: Twitter
Bugu da kari, Marigayin ya jagoranci tawagar ’yan sandan Majalisar Ɗinkin Duniya wajen sa ido kan zaɓe a Namibia, in ji rahoton Tribune Nigeria.
Bayan ritayarsa, ya shugabanci kwamitin shugaban ƙasa kan sake fasalin aikin ’yan sanda a Najeriya, sannan daga baya aka naɗa shi shugaban hukumar PSC.
Tsohon Sufetan Yan Sanda ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Sufeta Janar na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Solomon Ehigiator Arase ya rasu.
Rundunar yan sanda a Najeriya ta tabbatar da hakan, tana mai bayyana cewa Arase ya rasu ne a Asibitin Cedarcrest da ke birnin Abuja.
Sufeta Janar, Kayode Egbetokun ya kai ziyara ta’aziyya ga iyalan marigayin a Abuja, inda ya mika sakon jaje a madadin rundunar yan sanda
Asali: Legit.ng


