Gwamnatin Kano ta Dakatar da Malam Lawal Triumph daga Yin Wa'azi a Jihar
- Sheikh Lawan Triumph ba zai ci gaba da wa'azi ba a jihar Kano har sai ya kare kansa a gaban Majalisar Shura
- Wasu 'yan kungiyoyin dariku sun zargi Lawan da batanci ga Ma'aiki a cikin karatukansa da ya yi kwanan nan
- Sai dai, malamai da dama daga kungiyar Izala sun bayyana goyon bayansu tare da nuna tarayyarsu da malamin
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya ta dakatar da fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Lawan Shuaibu Abubakar watau Triumph daga yin wa'azi.
Wannan na zuwa ne bayan da aka samu sabani tsakanin malamin na Ahlus-sunnah da wasu daga cikin 'yan kungiyoyin dariku a jihar.

Source: Twitter
Dakatarwar na zuwa ne daga majalisar shura da gwamnatin Kano ta kafa, bayan da aka gabatar da wasu korafe-korafe game da salon wa'azin malamin.
Idan baku manta ba, an taba gurfanar da malamin darikar Qadiriyya, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara kan batanci ga Ma'aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin dakatar da Lawan Triumph
A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba 01 ga watan Oktoba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar.
A cewarsa, malamin na da bukatar kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman batanci ga Ma'aiki.
A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakinsa a matakin Majalisar ta shura.
'Ku koma gefe': Majalisar shura ga 'yan siyasa
Hakazalika, ya kuma yi kira ga 'yan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikinsa.
Ya kuma tabbatar da cewa majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da son rai ko rashin adalci ba.

Source: Facebook
Majalisar ta bayyana wadannan kalamai ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan batutuwan Malam Lawan.
Yadda batun Lawal Triumph ya faro
A wasu karatukansa, an ji malamin ya soki karamomi irinsu haihuwa da kaciya da kwalli da ake jinginawa Annabi Muhammad SAW.
Hakazalika, ya fassara was hadisai da Sufaye ke ganin hakan taba janibin Ma'aiki ne tare da nuna rashin da'a wajen yin bayanansa.
Wannan ya sa ake masa zargin ya ci mutuncin Ma'aiki tare da kwatanta shi da gama garin halittu ciki har da dabbobi da wadanda ba Musulmai ba.
Ba wannan ne karon farko da ake samun sabani tsakanin malamai ba a Najeriya, akan samu hakan a lokuta da dama.
Bayanan shugaban malaman Kano
A bangare guda, shugaban malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya yi tsokaci kan korafe-korafen da aka shigar kan maganganun Sheikh Lawal Abubakar Triumph.
Malamin ya bayyana cewa babu tabbacin cewa za a shawo kan rikicin malamai a Kano ta hanyar mukabala watau yin zama domin a baje hujjoji.
A bidiyon da Radiyon Premier ya wallafa a Facebook, Malamin ya ce kowa na ikirarin shi ne kan gaskiya, kowa na cewa yana kare addini, lamarin da ya ce ba zai kawo karshen rigimar ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

