PENGASSAN: Halin da Ake Ciki a NNPCL da NUPRC da NMDPRA bayan Fara Yajin Aiki
- Al'amura na neman tsayawa cak a fannin man fetur da iskar gas na Najeriya sakamakon yajin aikin da kungiyar PENGASSAN ta fara
- Yajin aikin ya kawo tsaiko a kamfanin NNPCL da sauran hukumomin da ke kula da harkokin man fetur da iskar gas
- Lamarin ya auku ne dai bayan an samu sabani tsakanin kungiyar PENGASSAN da matatar man Dangote
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Yajin aikin da kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta kasa (PENGASSAN) ta ayyana a ranar Litinin ya kawo tsaiko a kamfanin NNPCL da hukumomin NUPRC da NMDPRA.
Yajin aikin na PENGASSAN ya dakile ayyuka a muhimman hukumomin wadanda ke kula da harkokin man fetur da iskar gas na kasar nan.

Source: Facebook
An kulle ofisoshi saboda yajin-aikin PENGASSAN
Jaridar The Punch ta ce an kulle babbar kofar hedkwatar hukumar NUPRC da ke Abuja, lamarin da ya sa ma’aikata da dama suka tsaya a waje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’an tsaro da ke bakin aiki sun tabbatar da cewa babu ma’aikacin da aka bari ya shiga, bisa umarnin yajin aikin da kungiyar ta bayar.
Yajin aikin ya biyo bayan umarnin da majalisar zartarwa ta kasa ta kungiyar PENGASSAN ta bayar a karshen mako.
Umarnin ya sa mambobi a fadin kasar nan sun daina aiki, lamarin da ya jawo aka rufe muhimmam hukumomin da ke tafiyar da masana’antar man fetur da iskar gas ta Najeriya.
Abubuwa sun tsaya cak a NNPCL, NMDPRA
Haka nan, dukkan ayyuka a hedikwatar NMDPRA da ke cikin birnin Abuja sun tsaya cik, domin ma’aikata sun bi umarnin yajin aikin baki ɗaya.
Da yake tabbatar da halin da ake ciki, shugaban PENGASSAN a NMDPRA, Tony Iziogba, ya bayyana cewa kungiyar ta cin ma bin doka da kaso 100%, inda aka hana ma’aikata da baƙi shiga cikin ofisoshi.
Ya kara da cewa abokan aikinsa sun tabbatar da bin wannan doka a kamfanin NNPCL da sauran hukumomi masu alaka, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da labarin.
Meyasa PENGASSAN ta shiga yajin aiki?
PENGASSAN ta ce yajin aikin ya zama dole bayan korar ma’aikata kusan 800 a matatar man Dangote ba bisa ka’ida ba.
Ƙungiyar ta umarci a dakatar da kai danyen mai da iskar gas zuwa matatar Dangote, lamarin da ya girgiza bangaren makamashi na Najeriya.
'Yan kasuwar man fetur sun yi gargadin cewa hakan zai iya janyo gagarumar tangarda wajen rabon mai a kasar nan.
A ranar Lahadi, PENGASSAN ta bayyana tsunduma yajin aiki a fadin kasa baki ɗaya, inda ta umurci mambobinta a dukkan ofisoshi, kamfanoni, cibiyoyi da hukumomi da su daina aiki daga karfe 12:01 na safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Satumba, 2025.

Source: UGC
Haka kuma, kungiyar ta umurci mambobinta da ke wuraren aiki a filayen hakar mai da iskar gas cewa su ajiye aiki daga karfe 6:00 na safiyar ranar Lahadi, 28 ga Satumba, sannan su fara addu’o’i a kowane lokaci.
A halin yanzu dai hankali zai koma kan taron gaggawa da ministan kwadago ya kira bangarorin biyu a ranar Litinin.
PENGASSAN ta yi barazanar shiga yajin aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta kasa (PENGASSAN), ta yi barazanar fara yajin aiki.
Kungiyar ta yi barazanar ne bayan matatar Dangote ta kori ma'aikata sama da 800 daga bakin aiki..
Sakataren PENGASSAN na kasa ya yi zargin cewa matatar Dangote ta kori ma'aikatan ne saboda shiga kungiyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


