PENGASSAN: 'Abu 1 da Dangote Zai Yi don Hana Ƙarancin Fetur a Najeriya'
- PENGASSAN ta ce idan matatar man Dangote ta dawo da ma’aikatan da ta kora, rikicinsu zai kare cikin awa daya
- Kungiyar ta shiga yajin aiki tare da dakatar da isar da mai da iskar gas ga Dangote, bayan korar ma'aikata har 800
- Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo ya zargi Dangote da lalata tattalin arzikin Najeriya ta hanyar korar ma’aikata
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar manyan ma’aikatan man fetur, PENGASSAN, ta yi magana kan rikicin ta da matatar Dangote da ya sa ta tsunduma yajin aiki.
PENGASSAN ta ce za a kawo karshen rikicin ne kawai idan matatar Dangote ta maido da ma’aikatan da ta sallama kwanan nan.

Source: Getty Images
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta shiga yajin aikin gama-gari tun daga Lahadi, 28 ga Satumba, 2025, domin nuna adawa da korar wasu ma’aikata a matatar dake Lagos.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yajin aikin PENGASSAN da martanin Dangote
A cewar babban sakataren PENGASSAN, Lumumba Okugbawa, yajin aikin da suka shiga ya fara ne da rufe dukkan wuraren aiki na matatar Dangote.
Sannan an aika sakon umarni ga mambobin kungiyar a ofisoshi, hukumomi da kamfanoni a fadin Najeriya da su daina aiki daga karfe 12:01 na safiyar Litinin, 29 ga Satumba.
Kungiyar ta kuma dakatar da isar da danyen mai da iskar gas zuwa matatar Dangote da sauran cibiyoyin sinadaran fetur, kamar yadda muka ruwaito.
Sai dai kamfanin Dangote ya ce korar wasu ma’aikata da aka yi wani bangare ne na shirin garambawul a matatar mansa.
Matatar ta kuma zargi PENGASSAN da yunkurin lalata tsarin samar da makamashi a Najeriya ta hanyar katse wadannan kayayyaki.
PENGASSAN ta kare kanta daga zargin Dangote
A cikin hirarsa da tashar Channels TV, shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, ya ce matakin da Dangote ya dauka shi ne zai iya haddasa matsala ga tattalin arzikin Najeriya. Osifo ya ce:
“Mu a PENGASSAN muna maida hankali kan manufarmu. Kungiyarmu tana aiki a sama da kamfanonin mai da iskar gas 200 a Najeriya.
"Mu ne muke taka rawa wajen kawo kudaden shiga da ma tallafin musayar kudi da aka yi amfani da shi wajen gina matatar Dangote.”
Ya kara da cewa kungiyar ba za ta ja da baya ba idan har Dangote ya ki janye matakinsa.
“Idan har Dangote ya maido da mutanen da ya sallama yau, zan tabbatar muku da cewa komai zai dawo daidai cikin kasa da awa daya.” - Festus Osifo.

Source: Twitter
Sakon PENGASSAN ga matatar Dangote
Shugaban PENGASSAN ya kuma zargi matatar da yaudarar jama’a da kuma cutar da tattalin arzikin kasa saboda kawai ma’aikata sun nemi shiga kungiyar da ta kasance doka ta amince da ita.
“Ina tambaya, meya sa za ka kori mutane saboda kawai sun shiga kungiyar da take da rassa a ko’ina a masana’antar mai? Muna jiran Dangote ya amsa mana wannan tambayar."
- Festus Osifo.
Kungiyar ta ce ta shirya tsaf don warware rikicin nan take muddin aka yi adalci ta hanyar dawo da ma’aikatan da aka sallama.

Kara karanta wannan
Wahala ta kara tunkaro 'yan Najeriya sakamakon matakin da matatar Dangote ta dauka
Dangote ya daina sayar da mai da Naira
A wani labarin, mun ruwaito cewa, matatar man Dangote ta dakatar da shirin sayarwa ƴan kasuwa fetur a tsarin Naira.
Ƙungiyar IPMAN ta bayyana cewa dakatar da sayar da man fetur a Naira da Matatar Dangote ta yi, zai kara tsadar feturin a kasa.
Man fetur dai na cikin muhimmna abubuwan da yan Najeriya ke amfani da su, wanda tsadarsa ke jawo tsadar sufuri da farashin abinci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

