Ganduje Ya Taso Gwamna Abba a Gaba, Ya Fadi Kuskuren da Yake Yi a Gwamnatinsa
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi maganganu masu kaushi kan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Ganduje ya yi zargin cewa gwamnatin Gwamna Abba ba ta da masaniya kan harkokin mulki kuma tana kashe kudade kan ayyukan da ba su dace ba
- Tsohon shugaban na jam'iyyar APC, ya kuma bayyana cewa kudaden da Gwamna Abba ya samu cikin watanni shida, bai same su cikin shekaru takwas ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yi zargi kan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ganduje ya yi zargin cewa cikin watanni shida kacal, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu kudade daga asusun tarayya fiye da wanda ya samu a tsawon shekaru takwas da ya jagoranci jihar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Ganduje ya bayyana hakan ne bayan kammala wani taron masu ruwa da tsaki a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar rarraba kudi daga asusun tarayya ga jihohi na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Me Ganduje ya ce kan Gwamna Abba?
Da yake jawabi bayan kammala taron, Ganduje ya yi tambaya kan nasarorin da gwamnatin magajinsa ta samu.
Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf na kashe kudi ba bisa ka’ida ba.
"Lokacin da na hau kan mulki, ban bata lokaci wajen binciken wanda na gada ba. Mulki ba ya karewa da gwamnati guda. Amma Abba Yusuf ya fara mulkinsa da bincike."
"Ku gaya min, me suka gano? Sun samu kudi fiye da wanda na samu a shekaru takwas cikin watanni shida kacal. Amma me suka cin ma?”
“Wannan gwamnati ba ta da masaniya kan mulki. Kamar a kwatanta masinja da babban sakatare ne. Gwamnatinsu ta jahilci mulki, ba ta san inda ta dosa ba. Suna kashe kudi akan ayyukan da ba su da amfani.”
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje ya kuma yi wa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf lakabi da gwamnatin ramuwar gayya da rashin hangen nesa.
Ba a ji ta bakin gwamnatin Kano ba
An yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun bakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, bai mayar da martani kan tambayoyin da aka yi masa ba.

Source: Facebook
Karanta wasu labaran kan siyasar Kano
- Yadda Kwankwaso zai yi alaka da Ganduje idan ya koma APC da wasu abubuwa 2
- Ganduje ya hada Kwankwaso, Abba Kabir wuri guda, ya musu wankin babban bargo
- Da gaske Kwankwaso ya rubuta wasikar shiga APC? Madugun NNPP ya yi bayani
Gwamna Abba ya mika sunaye ga majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sunayen mutanen da yake so ya nada kwamishinoni a gwamnatinsa, ga majalisar dokokin jihar.
Gwamna Abba Kabir ya mika sunayen ne na mutum biyu ga majalisar dokokin don tantancewa da amincewa da su a matsayin kwamishinoni kuma mambobin majalisae zartarwar jihar.
Daga cikin mutane biyun da Gwamna Abba ya bada sunayensu, har da shugaban hukumar Kididdiga ta jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


