'Yan Bindiga Sun Kwashi Kashinsu a Hannu da Suka Shiga Wani Gari a Katsina
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi yunkurin sace mutane a karamar hukumar Danja ta jihar Katsina
- Miyagun sun kai farmakin ne a garin Dabai, inda suka yi yunkurin yin garkuwa da wasu mutane
- Jami'an tsaro sun yi artabu da 'yan bindigan inda suka samu nasarar fatattakarsu tare da kubutar da mutanen da suka sace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a garin Dabai da ke karamar hukumar Danja a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kai harin ta'addancin ne a daren ranar Asabar, 27 ga watan Satumban 2025.

Source: Twitter
Dan majalisar wakilai mai wakiltar Bakori da Danja, Hon Abdullahi Balarabe Dabai, ya tabbatar da kai harin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Garin Dabai nan ne mahaifar dan majalisar wakilai mai wakiltar Bakori da Danja da kuma dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar Danja, Shamsuddeen Abubakar Chiroma.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun cafke masu hada baki da 'yan bindiga dauke da kayan laifi a Katsina
'Yan bindiga sun sace mutane
Miyagun 'yan bindigan wadanda suka shigo cikin garin da misalin karfe 12:00 na dare sun yi awon gaba da wasu mutane.
Hakazalika 'yan bindigan sun harbi wasu mutane ciki har da kwamandan rundunar C-Watch na karamar hukumar Danja, a yayin harin.
Jami'an tsaro sun yi artabu da 'yan bindiga
Jami'an tsaro na 'yan sanda, C-Watch da CJTF sun yi musayar wuta da 'yan bindigan a yayin harin da suka kawo.
Hakizan jami'an tsaron sun samu nasarar kubutar da dukkanin mutanen da 'yan bindigan suka dauka domin tafiya da su.
Hakazalika, jami'an tsaron sun samu nasarar kashe dan bindiga guda daya da cafke wani guda daya tare da kwato mota daya a hannunsu.
An garzaya da mutanen da suka samu raunuka zuwa asibiti domin ba su kulawar da ta dace.
Wani mazaunin garin Dabai, Usman Sani, ya shaidawa Legit Hausa cewa 'yan bindigan sun shiga unguwarsu a yayin harin.

Kara karanta wannan
Abin ya yi muni: An bayyana sunayen malami da mutum 4 da suka 'mutu' lokaci Guda a masallaci
"Yan bindigan sun rabu gida biyu ne. Wasu sun shigo unguwarmu inda suka yi ta harbe-harbe. Sun zo ne daukar Alhaji Lawal mai taki. Sun sare shi da wuka amma ba su yi nasarar tafiya da shi ba."
- Usman Sani

Source: Original
Dan majalisa ya yi jaje
Hon. Abdullahi Balarabe Dabai ya jajantawa mutanen garin nasa bisa harin da 'yan bindigan suka kawo a daren ranar Asabar.
Dan majalisar wakilan ya kuma yabawa jami'an tsaro bisa namijin kokarin da suka yi wajen fatattakar 'yan bindigan.
"Innanillahi wa'inna'ilaihirraji'un!!! A madadina da iyalaina da dukkan magoya bayana Ina mika sakon jaje ga al'ummar mahaifata garin Dabai, a bisa iftila'i na 'yan bindiga da suka shigo cikin daren jiya."
"Jinjina ta musamman ga jami'an tsaro musamman jami'an tsaron C- watch/Civilian JTF. Muna addu'ar Allah yakiyaye afkuwar hakan a nan gaba, marasa lafiya Allah yabasu lafiya Amin ya Allah."
- Abdullahi Balarabe Dabai
'Yan sanda sun cafke masu hada baki da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an 'yan sanda sun samu nasarar cafke masu hada baki da 'yan bindiga a jihar Katsina.
'Yan sandan sun cafke mutanen ne guda biyu bisa zargin yunkurin kai man fetur ga 'yan bindigan.
Jami'an tsaron sun kama su ne a daidai lokacin da suke kokarin kai man fetur ga 'yan bindiga a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
