Kano: An Sanar da Abin da Maniyyata Za Su Biya don zuwa Aikin Hajjin 2026

Kano: An Sanar da Abin da Maniyyata Za Su Biya don zuwa Aikin Hajjin 2026

  • Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano, ta sanar da kudaden da maniyyata za su biya don zuwa aikin Hajji a kasa mai tsarki
  • Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Dederi, ya bayyana cewa mutanen da ke son zuwa aikin Hajji za su biya N8.2m
  • Hakazalika hukumar ta kayyade lokacin da maniyyata za su kammala biyan kudaden don samun gurbin zuwa aikin Hajjin shekarar 2026

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano, ta bayyana kudin da maniyyata za su biya don zuwa aikin Hajjin shekarar 2026.

Hukumar jin dadin Alhazan ta sanar da cewa maniyyata za su biya N8,244,813.67 a matsayin kudin zuwa aikin Hajjin shekarar 2026.

Hukumar jin dadin Alhazai ta Kano ta sanar da kudin aikin Hajji
Maniyyata na shirin hawa jirgin sama Hoto: @nigeriahajjcom
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sulaiman Dederi, ya fitar ranar Lahadi, 28 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Hukumar NAHCON ta rage kudin aikin Hajji na 2026 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nawa maniyyata za su biya a Kano?

Shugaban hukumar, Lamin Rabi’u Danbappa, ya tabbatar da cewa wannan kudin zai shafi dukkan masu niyyar zuwa aikin Hajji daga jihar Kano.

"Dukkan wadanda suka riga suka bada N8.5m za su samu ragin N255,186.33 bayan sun mika bukatar dawo da kudin a rubuce zuwa hukumar."

- Sulaiman Dederi

Sulaiman Dederi ya kara da cewa maniyyatan da za su fara biyan kudi dole ne su biya cikakken adadin N8,244,813.67.

Hakazalika ya bayyana an tsayar da ranar 31 ga Disamba, 2025, ta zama iyakar lokacin biyan kudi, kamar yadda hukumar NAHCON ta tsara.

An kuma bukaci dukkanin maniyyatan da su tabbatar sun kammala biyan kuɗin kafin wa’adin domin tabbatar da gurbin tafiyarsu.

A baya, shugaban hukumar, Alhaji Lamin Danbappa, ya tabbatar da kayyade N8.4m a matsayin kudin da NAHCON ta sanya ga masu niyyar zuwa aikin Hajjin 2026.

Hukumar ta bayyana cewa ta riga ta yi rijistar akalla Alhazai 3,155 domin aikin Hajjin 2026, kuma ta rufe sayar da guraben da aka warewa jihar.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Shugaban karamar hukuma a Bauchi ya yi bankwana da duniya

Kamar yadda aka saba kowace shekara, NAHCON ce ke tsara tafiyar Alhazai zuwa Saudiyya, yayin da hukumomin jihohi ke gudanar da rajista da sauran shirye-shirye.

An sanar da kudin aikin Hajjin 2026 da maniyyata za su biya a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan aikin Hajji

NAHCON ta rage kudin Hajjin 2026

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON), ta sanar da yin ragi a kudin zuwa aikin Hajjin shekarar 2026.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa ta cin ma matsayar rage kudaden ne bayan yin taro da masu ruwa da tsaki tare da samun amincewar gwamnatin tarayya.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana cewa ragin da aka yi, zai bada damar samun yin ibada ga al’ummar Musulmi da dama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng