Bayan yin garambawul, Gwamna Abba ya Mika Sunaye ga Majalisa don Nada Kwamishinoni

Bayan yin garambawul, Gwamna Abba ya Mika Sunaye ga Majalisa don Nada Kwamishinoni

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika da sunayen wasu mutane ga majalisar dokoki don nadaa su zama kwamishinoni a gwamnatinsa
  • Abba Kabir Yusuf ya mika sunayen ne ga majalisar domin tantancewa da tabbatarwa a matsayin kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwa
  • Mutanen biyu suna da kwarewa a fannonin da su ke aiki, kuma sun fito ne daga kananan hukumomin Bichi da Minjibir

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar.

Gwamna Abba ya mika sunayen ne domin tantancewa da tabbatarwa a matsayin kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwar jihar.

Gwamna Abba ya mika sunaye ga majalisar dokokin jihar Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Dr. Aliyu Isa Aliyu da Abdulkarim Maude Hoto: Sunusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook.

Gwamna Abba zai nada kwamishinoni

Wadanda aka zaba don zama kwamishinonin sun hada Abdulkarim Maude, mai neman zama SAN, wanda ya fito daga karamar hukumar Minjibir.

Kara karanta wannan

"Za a yi 'yar kure," An fara zama kan zargin Sheikh Triumph da taba mutuncin Annabi SAW

Abdulkarim Maude mai shekara 40 a duniya lauya ne wanda ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria.

Abdulkarim Maude yana da kwarewa a fannin harkokin ofis, zaman kotu, hulda da mutane da harkokin doka.

Na biyun shi ne Dr Aliyu Isa-Aliyu wanda yake 'Associate Professor' a fannin 'Allied Mathematics', wanda ya fito daga karamar hukumar Bichi.

Ya samu digirinsa na farko a fannin lissafi daga jami'ar Bayero (BUK) da ke Kano. Ya yi digirinsa na biyu a fannin lissafi daga jami'ar kimiyya da fasaha ta Jordan.

Hakazalika ya yi digirin digir a fannin lissafi daga jami'ar Firat da ke kasar Turkiyya.

‎Dr. Aliyu Isa Aliya ya fara aikin koyarwa a jami'ar tarayya da ke Dutse a shekarar 2014, ya samu karin girma zuwa babban lakcara sannan daga baya ya zama 'Associate Professor' a jami'ar North West da ke Kano.

Tun daga shekarar 2023, shi ne yake jagoranta hukumar kididdiga ta jihar Kano.

Dr. Aliyu mai shekara 41 yana daya daga cikin masu bincike a fannin lissafi a duniya, kuma yana daya daga cikin mutanen da su ka ci gajiyar shirin kai dalibai karatu zuwa kasashen waje na Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an kara samun gwamnan PDP da zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Hakazalika, ya taba zama sakataren kudi na jam'iyya NNPP reshen jihar Kano.

Gwamna Abba zai nada kwamishinoni
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Gwamna Abba ya yi garambawul a gwamnatinsa

Mika sunayen dai na zuwa ne bayan Gwamna Abba ya yi garambawul a gwamnatinsa.

Gwamnan dai ya sauyawa wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa wuraren aiki. Daga cikin wadanda abin ya shafa har da kwamishinan shari'a, Barista Haruna Isa Dederi.

Gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatun dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta bayar da tallafin karatu ga 'yan asalin jihar.

Gwamnatin ta bayar da tallafin karatun digiri na biyu ga dalibai 240 'yan asalin jihar don zurfafa karatunsu.

An dai dauki nauyin daliban ne domin yin karatu a jami'o'i masu zaman kansu da su ke a jihohi daban-daban na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng