Gwamnatin Kano Ta Faɗi Barazanar da Kwamishinan Yan Sanda Ya Jefa Abba Kabir

Gwamnatin Kano Ta Faɗi Barazanar da Kwamishinan Yan Sanda Ya Jefa Abba Kabir

  • Lauyan Gwamnatin Kano, AbdulKarim Maude, ya yi karin haske kan rashin ganin yan sanda a bikin ranar yanci da aka yi a jihar
  • Maude ya ce janye ‘yan sanda daga filin biki na ’yancin kai ya jefa Gwamna Abba Yusuf cikin barazanar tsaro
  • Ya zargi kwamishinan yan sanda, Ibrahim Bakori da tauye ikon gwamna a matsayin babban jami’in tsaro na jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnatin jihar Kano ya bayyana damuwa kan matakin Kwamishinan yan sanda a ranar bikin yancin kai a makon jiya.

Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, AbdulKarim Maude, ya ce janye ‘yan sanda ya haifar da barazanar tsaro ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Gwamnatin Abba ta taso Kwamishinan yan sanda a gaba
Kwamishinan yan sanda, Ibrahim Bakori da Gwamna Abba Kabir. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Zargin da ake yi ga Kwamishinan yan sanda

Hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Mai Mala Buni ya gwangwaje dan tsohon gwamna da mukami a gwamnatinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maude ya zargi kwamishinan yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori da take ikon Gwamna a matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar.

Ya ce halin da aka samu kai a cikin lamarin ya nuna cewa CP ya karya ikon zartarwa na Gwamna tare da jefa shi cikin barazanar tsaro.

Yan sanda: Matsalar rashin bin umarnin Abba Kabir

Lauyan ya jaddada cewa dole ne Kwamishinan ya bi umarnin Gwamna a dukkan lamuran tsaro da zaman lafiya sai dai idan shugaban kasa ya bayar da sabanin umarni.

Ya ce:

"Dole ne kwamishinan ya bi umarnin doka na Gwamna a harkokin zaman lafiya da tsaro sai idan Shugaban Kasa ya bayar da sabanin umarni."

Ya ce rashin bin umarnin Gwamna ba tare da sanar da shugaban kasa ba ya karya daidaiton kundin tsarin mulki da ke cikin sashe na 214/215.

Ana takun saka tsakanin Abba Kabir da Kwamishinan yan sanda
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Bankadar da wani dan sanda ya yi

Wani jami’in ‘yan sanda da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce dukkan shugabannin tsaro hudu ne ba su halarci bikin ’yancin kai ba saboda rashin jituwa da Gwamna.

Kara karanta wannan

Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi

Jami’in ya kara da cewa Gwamna Abba Kabir bai da kwanciyar hankali da rundunar ‘yan sanda saboda irin matsayinsu a shari’o’in siyasa da suka shafi shi da abokan adawarsa.

A cewarsa:

“Saboda wannan rashin jituwar, wani lokaci Gwamna kan ƙi ɗaga wayar ko karanta saƙon CP, wani lokaci kuma yana tura mu’amalarsa ga ƙananan ma’aikata."

Ya ce matsalar ta fi batun bikin, domin Gwamna ya ki karbar bakuncin Kwamishina da AIG Zone 1 duk da cewa sun yi ta kokarin kai masa ziyara.

An kama wanda ya sace basarake a Kano

Mun ba ku labarin cewa yan sanda sun kama matashi dan shekara 27 da ake zargi da hannu a garkuwa da Dagacin Garun Babba a shekarar 2023.

Matashin wanda aka fi sani da Yellow ya amsa cewa su suka sace basaraken, ya fara jero sunayen duka masu hannu a lamarin.

Rundunar yan Sandan Kano ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.