Abin Tausayi: Gwamna Ya Shiga Yanayi, Rayuwarsa Ta Canza bayan Rasuwar Matarsa
- Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya ce ya shiga cikin mawuyacin hali tun bayan rasuwar matarsa, Patience Eno a bara
- Ya bayyana cewa wasu lokutan ya kan ji kamar tafiya ta yi kawai amma za ta dawo, wasu lokutan kuma yana jin kamar tana tare da shi
- Umo Eno ya ce yana shafe tsawon lokaci a ofis ba don yana son hakan ba, sai dan babu mai kula da shi idan ya koma gida
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom, a ranar Juma’a, ya bayyana yadda rayuwarsa ta sauya bayan mutuwar matarsa, Misis Patiece Eno.
Gwamna Eno ya ce mutuwar matarsa ta sanya shi cika wa kansa aiki, inda yake shafe sa'o'i fiye da kima a ofis yana gudanar da aiki.

Kara karanta wannan
'Yar Najeriya da ta shirya kafa tarihin kwanciya da maza 100 a awa 24 ta canza shawara

Source: Facebook
Ya bayyana haka ne a wurin bikin cika shekara guda da rasuwar Uwargidan Gwamnan Akwa Ibom, wanda aka yi a birnin Uyo, in ji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rayuwar Gwamna Eno ta sauya
Ya ce rashin matarsa ya taba rayuwarsa matuka, yana mai cewa dole yake zama yana aiki har tsakar dare domin cike gibin rashinta a kusa da shi.
Gwamnan ya jaddada cewa aiki ya zama wata hanya ta rage radadin rashin matarsa wadda ta rasu a ranar 26 ga Satumba, 2024.
Cikin murya mai rauni da abin tausayi, Gwamna Eno ya ce:
"Ba na tunanin zan samu wata mata da ta fi marigayiya a rayuwata, ita ce ginshikin iyalina, ta kware wajen tafiyar ta gida, tana kare ni har a gaban yaranmu."
"A tsawon shekaru 40 da muka yi tare, ba a taba shiga tsakaninmu ko da nufin sulhu ba. Zaman da nake a ofis har tsakar dare, ba ina son cika ma kai na aiki ba ne, babu wacce za ta kira ni ta ce ka dawo gida haka nan.
"Ina kewar yadda take kira na ta ce maigida ka dawo gidan haka nan, aikin nan ba zai kare yau ba, ina nan ina jiranka. Ji nake kamar tayi tafiya ne, ina jiran ta dawo."
Jiga-jigai sun halarci bikin tunawa da matar Eno
Gwamnan ya ce a wasu lokuta yana jin kamar har yanzu tana tare da shi, yana mai bayyana yadda ya ji kamar ita ta zaba masa rigar da ya sa lokacin da ya kammala digiri na uku a Jami'ar Uyo.
Bikin tunawa da rasuwar matar gwamnan ya samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma.

Source: Facebook
Haka zalika matan gwamnonin jihohin Legas, Enugu da Imo, da kuma wasu manyan baki sun halarci bikin da aka shirya, Daily Post ta ruwaito.
Gwamnatin Eno ta ayyana dokar ta-baci
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Akwa Ibom ta ayyana dokar ta-baci a fannin kiwon lafiya bayan kammala nazari kan tsarin ci kiwon lafiya a jihar.
Gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Umo Eno ya ce wannan matakin zai taimaka wajen daukar matakan da suka dce don ceto bangaren lafiya.
Kwamishinan labarai, Elder Aniekan Umanah, ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jihar Akwa Ibom.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

