An Yi Rashi: Shugaban Karamar Hukuma a Bauchi Ya Yi Bankwana da Duniya

An Yi Rashi: Shugaban Karamar Hukuma a Bauchi Ya Yi Bankwana da Duniya

  • Mutuwa ta dauki daya daga cikin shugabannin kananan hukumomin jihar Bauchi, bayan ya yi fama da rashin lafiya
  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya aika da sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar Hon. Yakubu Garba Tela, a ranar Asabar, 27 ga watan Satumban 2025
  • A cikin sakon ta'aziyyar da gwamnan ya fitar, ya bayyana halayen kirki na marigayin wadanda za a rika tuna shi da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Allah ya yi wa daya daga cikin shugabannin kananan hukumomin jihar Bauchi rasuwa.

Shugaban karamar hukumar Dambam a jihar Bauchi, Hon. Yakubu Garba Tela, ya yi bankwana da duniya.

Shugaban karamar hukuma ya rasu a Bauchi
Shugaban karamar hukumar Dambam, marigayi Yakubu Garba Tela Hoto: Zakar Muhammed
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa Hon. Yakubu Garba Tela ya rasu ne a ranar Asabar bayan gajeruwar rashin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC) ta ba Yakubu Garba Tela takardar shaidar lashe zaɓe a ranar 18 ga watan Agusta, 2024, tare da sauran shugabannin kananan hukumomi 19 a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Hadimin Gwamna Bago ya yi bankwana da duniya

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ta bakin mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya yi alhinin rasuwar.

Gwamna Bala ya yi ta'aziyya

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana rasuwar shugaban karamar hukumar a matsayin abin bakin ciki, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da labarin.

Hakazalika gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, al’ummar karamar hukumar Dambam, shugabannin kananan hukumomi, da kuma daukacin jama’ar jihar Bauchi.

Ya bayyana marigayi Yakubu Garba Tela a matsayin bawan Allah mai jajircewa a hidimar jama’a, mai kwazo wajen wayar da kan al’umma.

Gwamnan Bauchi ya yi ta'aziyyar shugaban karamar hukuma
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Haka kuma ya bayyana shi a matsayin jagora na gari wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ci gaban jama’arsa da karamar hukumar Dambam.

Gwamna Mohammed ya ce za a dade ana tunawa da marigayin saboda natsuwarsa, kishinsa wajen aiki, da kuma abubuwan da ya yi wa jama'arsa.

Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya ba shi hutu na har abada, sannan ya ba iyalansa, abokanansa da jama’ar Bauchi hakuri da juriyar jure wannan rashi mai raɗaɗi.

Kara karanta wannan

Sarki ya kinkimo bukatar kirkiro jiha 1, ya fadawa Tinubu gaba da gaba a Ibadan

Karanta wasu labaran kan jihar Bauchi

Daliba ta rasu a kwalejin Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa an shiga jimami a jihar Bauchi bayan rasuwar wata daliba a kwalejin fasaha ta tarayya da ke shirin kammala karatunta.

Dalibar mai suna Barira Adam wadda ke aji na biyu a fannin koyon aikin jarida ta rasu ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Satumban 2025.

Hukumar kwalejin wadda ta tabbatar da rasuwar dalibar ta bayyana cewa ta rasu ne a dakin kwanan dalibai da ke harabar makarantar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng