An Shiga Jimami bayan Ramin Hakar Ma'adanai Ya Rufta da Mutane Sama da 100 a Zamfara
- Mummunan ibtila'i ya ritsa da wasu mutanen da suka fita zuwa wajen aikin hakar ma'adanai a jihar Zamfara
- Lamarin ya auku ne bayan da wani ramin haka ma'adanai ya rufta kan ma'aikata a karamar hukumar Maru, wanda hakan ya jawo asarar rayuka
- Majiyoyi sun bayyana cewa akwai sama da mutane 100 a cikin ramin hakar ma'adanan lokacin da ya rufta musu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Ana fargabar fiye da mutum 100 sun mutu sakamakon ruftawar wani ramin hakar zinare a jihar Zamfara.
Mutanen da suka tsira daga lamarin da kuma mazauna yankin su ka bayyana hakan.

Source: Original
Jaridar The Nation ta ce lamarin ya auku ne a wani rami da ke wajen hakar ma’adanai na Kadauri, a karamar hukumar Maru.
Rami ya ruguje da mutane a Zamfara
Ramin ya ruguje ne a ranar Alhamis yayin da daruruwan ma’aikatan hakar ma’adanai ke aiki a karkashin kasa.
Rahotanni sun bayyana cewa ana ci gaba da aikin ceto har zuwa daren jiya Juma'a.
Sanusi Auwal, Wani mazaunin yankin da ya shiga cikin aikin ceto, Sanusi Auwal, ya bayyana cewa an riga an fitar da gawarwaki akalla 13 daga cikin ramin da ya ruguje, ciki har da na ɗan uwansa.
"Fiye da ma’aikatan hakar zinare 100 ne ke cikin ramin lokacin da ya ruguje."
- Sanusi Auwal
Wani wanda ya tsira, Isa Sani, wanda ke samun kulawar likitoci saboda raunukan da ya samu, ya bayyana cewa Allah ne ya kubutar da su.
"Mun yi sa’a da aka ceto mu da ranmu. Daga cikin fiye da mutum 100, mu 15 ne kawai aka ciro da ransu."
- Isa Sani
Wasu mutane sun tsira daga ramin
Wani ganau, Sani Hassan, wanda ya sha da kyar, ya shaidawa jaridar Punch cewa yana daga cikin wadanda suka samu sa'ar tsira da ransu.
A cewarsa, yana aikin hakar zinare ne a cikin ramin a ranar Alhamis lokacin da ya fito don shan ruwa.
"Jim kaɗan bayan na fito daga ramin hakar zinaren, sai kawai ya ruguje yayin da abokan aikina da dama ke ciki."
- Sani Hassan
Mai magana da yawun ‘yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, bai amsa kira da sakonnin da aka tura masa domin jin ta bakinsa ba.

Source: Facebook
Karanta wasu labaran kan hakar ma'adanai
- Gwamnatin tarayya ta dage haramcin hakar ma'adanai a Zamfara, ta fadi dalili
- Lauya ya nuna yatsa ga gwamna kan hana hakar ma'adanai a Arewa
- An shiga jimami yayin da ramin hakar ma'adanai ya rufta kan mutane a Arewa
'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun kai harin ne a wani kauye mai suna Bayan Dutsi da ke yankin Tofa a karamar hukumar Bungudu ta jihar.
Tsagerun 'yan bindigan sun jikkata mutane uku tare da yin awon gaba da wasu mutane da dama wadanda ba a san adadinsu ba a yayin harin.
Asali: Legit.ng

