"Za a Yi 'Yar Kure," An Fara Zama kan Zargin Sheikh Triumph da Taba Mutuncin Annabi SAW

"Za a Yi 'Yar Kure," An Fara Zama kan Zargin Sheikh Triumph da Taba Mutuncin Annabi SAW

  • Kwamitin Shura na jihar Kano ya fara zama kan korafe-korafen da jama'a suka shigar kan Sheikh Lawal Abubakar Triumph
  • Wannan zama na zuwa ne bayan gwamnatin Kano ta hannun sakatarenta ta mika duk korafe-korafen ga kwamitin don yin abin da ya dace
  • Kwamitin ya bayyana cewa zai gayyaci masu korafi da Sheikh Triumph domin bai wa kowane bangare damar gabatar da hujjoji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Kamar yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawari, gwamnatin Jihar Kano ta mika ƙorafe-ƙorafen da aka shigar kan Sheikh Lawal Abubakar Triumph ga Kwamitin Shura.

Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) ne ya mika ƙorafe-ƙorafen zuwa ga kwamitin a ranar Juma’a domin fara tattaunawa kan zargin malamin da taba mutuncin Manzon Allah SAW.

Sheikh Lawal Abubakar Triumph.
Hoton babban malamin Sunnah a Kano, Sheikh Lawal Abubakar Triumph Hoto: Sheikh Lawal Abubakar Shu'aib Triumph
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya ce kwamitin ya fara zama kan wadannan korafe-korafe domin daukar matakin da ya dace bisa tanadin shari'ar Musulunci.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a ba Sheikh Triumph damar bada hujjoji

A zaman farko da kwamitin ya yi, ya cimma matsayar cewa za a gayyaci wadanda suka kawo korafi da Sheikh Triumph domin ba kowa damar gabatar da hujjoji.

A cewar kwamitin, a musulunci ba a tabbatar da tuhuma sai an ba kowane bangare damar gabatar da hujjojinsa, hakan ya sa za a gayyaci Sheikh Triump ya kare kansa.

Sakataren kwamitin, Shehu Wada Sagagi, wanda ya zanta da manema labarai bayan zaman, ya ce an tsara hakan ne domin tabbatar da adalci.

“Bayan mun saurari kowane bangare, kwamiti zai tattauna sannan ya ba da shawararwari ga gwamnatin Kano,” in ji shi.

Kwamitin Shura ya ja hankalin jama'ar Kano

Ya tabbatar da cewa wasu daga cikin masu ƙorafin sun yi barazanar daukar matakin shari'a, amma ya roƙe su da su bari a kammala tsare-tsaren da kwamitin shura ya yi.

“Muna kira ga jama’a da su ci gaba da zama lafiya. Kano na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ake zaune lafiya.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun nemi saka dokar batancin Annabi SAW a Kano

"Ya rataya a wuyanmu gaba ɗaya mu kare wannan zaman lafiya domin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma."
“Wannan kwamitin ya ƙunshi manyan malamai masu zurfin ilimin shari’ar Musulunci. Za mu ba gwamnati shawarar da ta dace kan wannan lamari, in sha Allah.”

- Shehu Wada Sagagi.

Kwamitin Shura da Sheikh Lawal Triumph.
Hoton lokacin da Sakataren Gwamnatin Kano ya mika korafe-korafe kan Malam Triumph ga kwamitin shura Hoto: Sheikh Lawal Abubakar Shu'aib Triumph
Source: Facebook

Kwamitin ya yaba wa gwamnatin Kano bisa yadda ta mika al’amarin domin a warware shi cikin tsarin Musulunci maimakon barin ya rikide zuwa tashin hankali, in ji rahoton Daily Nigerian.

Daga cikin zarge-zargen da ake wa Malam Triumph akwai kalaman da ya yi kan haihuwar Fiyayyen Halitta da kaciya da na iyayen Annabi, lamarin da wasu ke ganin ya taba mutuncin Manzon Allah SAW.

Malaman Sunnah sun kai nasu korafin a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa malaman Sunnah a jihar Kano sun shigar da korafi a ofishin gwamnatin jihar Kano kan mutanen da ke ikirarin batanci ga Annabi SAW.

Malaman masu da’awar Sunnah a jihar Kano sun nemi gwamnatin jihar da ta kafa doka ko ka’ida kan ikirarin zargin batanci ko zagin Annabi (SAW).

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano za ta dauki mataki kan malamin da ake zargi da taba mutuncin Manzon Allah SAW

A cewarsu, malamai ne suka dace su tabbatar da ko wani abu ya kai ga batanci ga fiyayyen halitta ko a’a kafin a dauki mataki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262