NiMet: Ruwa da Tsawa za Su Shafi Harkokin Jama'a a Kano, Wasu Jihohin Arewa
- Hukumar NiMet ta bayyana cewa za a samu hadari da ruwan sama a wasu jihohin Arewa da Kudu ranar Asabar, 27, Satumba, 2025
- An yi gargadin cewa hadarin na iya kawo tsaiko ga harkokin zirga zirga da kuma iya jawo a kan titunan wasu jihohin
- Hukumar ta shawarci al’umma musamman mazauna jihohin da aka ayyana da su dauki matakan kariya daga ambaliyar da za ta iya faruwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, wato NiMet, ta fitar da hasashen yanayi na ranar Asabar, 27, Satumba, 2025, wanda ya shafi sassan Arewa da Kudu.
Hasashen hukumar ya nuna cewa za a samu hadari da ruwan sama matsakaici a wurare da dama a fadin kasar.

Source: Twitter
Hukumar NiMet ta fitar da sanawa kan hasashen yanayin ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta kuma yi gargadi ga jama’a da masu abubuwan hawa da su kasance cikin shiri wajen kaucewa matsalolin da ruwan sama ka iya haifarwa.
Za a yi ruwa da guguwa a jihohi
A safiyar Asabar, sassan jihohin Arewa za su fara da yanayi mai hadari tare da fitowar rana lokaci zuwa lokaci. Sai dai da yamma zuwa dare, ana sa ran mamakon ruwa hade da tsawa da araduwa.
Jihohin da abin zai fi shafa sun hada da Adamawa, Taraba, Yobe, Jigawa, Gombe, Bauchi, Kano, Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi.
Hakan na iya shafar harkokin sufuri da kasuwanci a wadannan yankuna, musamman ga manoma da kuma masu safarar kaya.
Yanayi a sauran jihohin Arewa da Abuja
Haka zalika, wasu jihohin Arewa kamar Niger, Kwara, Benue, Kogi, Plateau, Nasarawa da Babban Birnin Tarayya na Abuja za su fara da hadari da dan hasken rana a safiya.
Sai dai da tsakar rana, an yi hasashen ruwan sama tare da guguwa za su sauka a wadannan wurare.

Source: Twitter
NiMet ta jaddada cewa duk wanda zai yi tafiya musamman ta hanya ya tabbatar da an dauki matakan kariya.
Hasashen yanayi a jihohin Kudu
Ga jihohin Kudu, safiyar Asabar za ta kasance da hadari da kuma dan ruwan sama a wasu wurare, yankunan da abin ya shafa sun hada da Oyo, Ogun, Ondo, Lagos, Edo, Delta da Bayelsa.
Da yamma zuwa dare, ana sa ran ruwan sama tare da hadari ya zuba a mafi yawan sassan yankunan Kudu gaba daya.
Wannan na iya kawo tsaiko ga harkokin sufuri, musamman a birane masu cunkoso kamar Legas da kuma sauran garuruwa da ke bakin teku.
NiMet gargadi jama'a kan ruwan sama
A wani rahoton, kun ji cewa NiMet ta yi gargadin cewa ruwan sama mai karfi na iya kawo tsaikon ayyuka a Kano, Taraba da wasu jihohin Arewa.
Hukumar ta shawarci jama’a da ke zaune a wuraren da ruwa kan taru da su dauki matakan kariya domin kaucewa hatsarin ambaliya.
Haka kuma ta bukaci hukumomin ba da agajin gaggawa da sauran hukumomin da abin ya shafa da su kasance cikin shiri don bada agaji idan bukatar hakan ta taso.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


