Yajin Aiki: Gwamnati Ta Yi Hobbasa, Ta Dakile Barazanar Rashin Wuta a Najeriya

Yajin Aiki: Gwamnati Ta Yi Hobbasa, Ta Dakile Barazanar Rashin Wuta a Najeriya

  • An dakatar da yajin aikin ma’aikatan wutar lantarki bayan sa’o’i 10, wanda ya hana fuskantar matsanancin rashin wuta a fadin ƙasar
  • Ma’aikata da gwamnatin tarayya sun cimma yarjejeniya a wani taron gaggawa da aka gudanar a Abuja bayan barazanar ma'ikatan
  • Kungiyoyin kwadago sun ce sun dakatar da yajin aiki ne amma za su dawo da shi idan gwamnati ko TCN suka karya alkawari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jama'a sun samu sa'ida a Najeriya a ranar Alhamis, bayan da ma’aikatan kamfanin raba wutar lantarki na Najeriya (TCN) suka dakatar da yajin aikin da suka fara.

Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) da Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Ma’aikata na Kamfanonin Lantarki (SSAEAC), ne su ka yi barazanar yajin aiki.

Kara karanta wannan

Bulama Bukarti ya hango matsaloli a sulhu da ƴan ta'adda, ya ba gwamnati shawara

Ma'aikatan wuta sun dakatar da yajin aiki
Hoton gari a duhu, jami'in kamfanin wutar lantarki Hoto: @officialABAT, @TCN_NIGERIA
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce sun dakatar da yajin ne bayan sa’o’i 10 na tattaunawa da jami’an gwamnatin tarayya a wani taron gaggawa da aka gudanar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatan wutar lantarki sun zauna da gwamnati

Daily Post ta ruwaito cewa ta ruwaito cewa taron ya samu halartar wakilai daga Ma’aikatar Wutar Lantarki, Ma’aikatar Kwadago da Ayyuka, shugabannin TCN, da sauransu.

Sanarwar hadin gwiwa da aka fitar bayan taron ta bayyana cewa an amince da sake nazarin rahoton kwamitin da ke duba batutuwan da suka janyo yajin aiki.

Ana sa ran a kammala nazarin cikin ranakun 6 zuwa 7 ga Oktoba 2025, kafin a fara aiwatar da matakan warware matsalolin.

TCN da NISO za su yi hadin gwiwa wajen lissafa yawan kuɗin da za a kashe don cika shawarwarin kwamitin, tare da gabatar da shirin aiwatarwa ga Ministan Wuta da kungiyoyin kwadago.

An kuma bukaci hukumar kula da farashin wuta ta NERC da ta hanzarta bita kan tsarin farashi don a cimma matsaya da daidaito.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Gwamnatin katsina ta gano ma'aikatan bogi sama da 3,000

Ma'aikatan wuta sun fasa yajin aiki

Yarjejeniyar ta kuma tanadi cewa babu wani ma’aikaci da za a hukunta saboda shiga yajin aikin da kungiyoyin za su kira.

Wannan ne ya sa kungiyoyin kwadago suka dakatar da yajin aikin, amma suka jaddada cewa za su koma yajin aiki idan an saba yarjejeniyar.

Gwamnati ta shiga tsakani a kan tafiya yajin aiki
Hoton turakun wutar lantarki, gari a duhu Hoto: Getty
Source: Getty Images

Kungiyoyin kwadagon sun bayyana wannan ci gaban a matsayin babbar nasara, amma suka gargadi gwamnatin da kada ta yi wasa da alkawarin da aka ɗauka.

Yajin aikin da aka fara a ranar Laraba ya samo asali ne daga koke-koken rashin biyan albashi tun watan Afrilu, rashin kayan aiki da tsaro, da kuma rashin biyan haƙƙin masu ritaya.

Wutar lantarki ta samu matsala

A baya, mun wallafa cewa turakun wutar lantarki sun kara lalacewa a Najeriya, lamarin da ya jefa al’umma cikin duhu a ko’ina a fadin kasar nan a yayin da ake fama da karancinta a wasu wuraren.

Rahotanni daga hukumar ISO sun nuna cewa karfin samar da wuta ya sauka daga megawatt 2,917.83 zuwa kusan megawatt 1.5 a safiyar ranar Asabar, 10 ga watan Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: SSANU, NASU sun kara wa gwamnatin Tinubu lokaci

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya fito fili ya tabbatar da cewa yankunansu sun fada cikin wannan matsala ta katsewar wuta, inda jama'a su ka fada a duhu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng