An Shiga Jimami bayan Tsintar Gawarwakin Wasu Yaran Masoyin Gwamna Zulum

An Shiga Jimami bayan Tsintar Gawarwakin Wasu Yaran Masoyin Gwamna Zulum

  • Wani mummunan lamari ya faru a jihar Borno bayan tsintar gawar wasu yara a safiyar ranar Alhamis
  • Wasu daga cikin yaran dai 'ya'ya ne ga wani mai goyon bayan Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno
  • Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta fara gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - An shiga jimami a jihar Borno bayan tsintar gawar 'ya'yan wani mai goyon bayan Gwamna Babagana Umara Zulum.

An tsinci gawar yaran guda uku ciki har da yara biyu na Zannah Jaridama Bornoye da kuma ɗan makwabcinsa.

An tsinci gawarwaki yaran masoyin Gwamna Zulum
Hoton Zannah Jaridama Bornoye tare da yaronsa da Gwamna Babagana Umara Zulum Hoto: Zanna Jaridama Bornoye, Dauda Iliya
Source: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masoyin Zulum ya soki jami'an gwamnati

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan Jaridama ya fito fili ya soki wasu manyan ’yan siyasa da ake zargin suna kusa da Gwamna Zulum.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama malamim addinin musulunci a jihar Bauchi

A cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, Jaridama ya zargi wasu daga cikin manyan da ke kewaye da gwamnan da amfani da shi don samun abin duniya.

Ya yi zargin cewa suna tara dukiya ta hanyar kwangila, mukamai, da kuma amfani da dukiyar gwamnati.

Ya yi tir da cewa yayin da Gwamna Zulum ke ɗaukar nauyin ayyuka da jagorancin gwamnati, waɗanda ke ikirarin goyon bayansa sun fi sha’awar kwangila, manyan gidaje, da tara kuɗaɗe.

“Suna sanya manyan kaya suna bin shi ko’ina, amma idan lokacin kare shi ya yi, sai a neme su a rasa. Munafukai ne. Duk wani bikin aure, Zulum. Kuɗin makaranta, Zulum, gidaje, Zulum. Me kuke kawowa ga jama’a?"

- Zannah Jaridama Bornoye

Jaridama ya ci gaba da cewa wasu daga cikin mutanen sun shiga gwamnati da abin hawa guda ɗaya, amma yanzu sun tara ɗimbin dukiya, duk da haka ba za su iya kashe miliyan ɗaya ba don kare mutuncin gwamnan.

An tsinci gawarwakin yaran Jaridama

Sai dai, wani ibtila'i ya auku cikin awa 24 bayan wannan magana. ’Ya’yansa biyu, Mama, yarinya mai shekara 14 da kuma Anwar, yaro ɗan shekara biyu da wata huɗu, sun ɓace lokacin da suke wasa a gaban gidansu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka dan sanda, an yi awon gaba da jami'an tsaro

A cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook, Jaridama ya yi kira da a taimaka masa wajen nemo yaran, inda ya yi alkawarin mika kansa a matsayin fansa idan hakan zai ceci rayuwar ’ya’yansa.

"Ina baran addu'a daga wajen kowa da kowa. Ni ake nema ba yarana ba. Zan zo duk inda suke kar ku salwantar da rayuwarsu, yara ne ba su san komai ba."
"Jama'a dan Allah ku taimaka min da addu'a ni ban damu da rayuwata ba amma ku tausayawa wannan kananan yaran ni ake bukata. Wallahi Tallahi zan zo duk suke ni in zama fansan rayuwarsu. Su har yanzu hara ne amma ni na yarda zan bada kai na a kashe ni, a bar wadannan kananan yaran su ci gaba da rayuwa."

- Zanna Jaridama Bornoye

Sai dai, da safiyar ranar Alhamis, an gano gawar yaran guda uku a cikin bayan ɗaya daga cikin tsofaffin motocinsa da ke cikin gidansa.

Wani abin ibtila'i ya auku a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Kwamishinan ’yan sanda na jihar Borno, Nazir Abdulmajid, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun je wurin, sun ɗauki hotuna, sannan sun kai gawarwakin zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri domin yin bincike.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jigawa ya bayyana matsayarsa kan tazarcen Tinubu a 2027

Ya ce har yanzu ba a tabbatar ko sace su aka yi sannan aka kashe ba, ko kuma yaran sun shiga bayan motar ne sannan suka kulle kansu, lamarin da ya jawo mutuwarsu.

"A yanzu ba za mu iya cewa ga abin da ya faru ba, kuma ba za mu iya tabbatar da cewa lamarin yana da nasaba da siyasa ba. Bincike ne zai nuna gaskiya."

- Nazir Abdulmajid

'Yan ISWAP sun yi barna a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan kungiyar ISWAP sun kai wani harin ta'addanci a jihar Borno.

'Yan ta'adan na ISWAP sun kashe shugaban kungiyar mafarauta a harin da suka kai a karamar hukumar Damboa.

Miyagun 'yan ta'addan sun hallaka shugaban mafarautar ne bayan sun yi awon gaba da shi a gidansa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng