'Kirista ne amma Ya Cancanci Aljanna,' El Rufa'i Ya Yi wa Ogbeh Addu'ar Rahama
- Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi niyyar naɗa Audu Ogbeh a matsayin sakataren gwamnati
- Ya ce Buhari ya ci burin haka ne domin ya nuna adalci da kuma kawar da zargin nuna bambancin addini da kin jinin wasu kabilu
- El-Rufa’i ya jaddada cewa zai cigaba da rokon Allah ya ba Audu Ogbeh Aljanna saboda ya yi rayuwa mai kyau a lokacin da ya ke raye
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana yadda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fasa naɗa marigayi Audu Ogbeh a matsayin sakataren gwamnatin tarayya (SGF).
Tsohon gwamnan Kaduna ya bayyana cewa wasu abubuwa ne suka faru Muhammadu Buhari ya fasa nada Audu Ogbeh a wannan kujera.

Source: Facebook
A wani bidiyo da Nasir El-Rufa'i ya yi bayani a YouTube, ya bayyyana cewa zai cigaba da rokon Allah ya ba marigayin Aljanna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Managar El-Rufa'i kan Buhari da Ogbeh
A cewar El-Rufa’i, tun bayan zaben shekarar 2015, wani abokinsa ya nemi ya shiga tsakani domin ya taimaka masa ya samu mukamin SGF.
Bayan ya ziyarci Buhari a matsayin zababben shugaban kasa, ya ce masa ya riga ya yanke shawarar nada wani daga yankin Arewa ta Tsakiya.
El-Rufa’i ya ce:
"Na tambaye shi, wa kake tunanin nadawa?' Sai ya ce, ‘Audu Ogbeh. Shi ne zabina,’"
El-Rufa'i ya ce ya yi martani da cewa:
"Zabi nagari ne sosai, Allah ya taimaka."
Dalilin hana Ogbeh mukamin SGF
El-Rufa’i ya ce daga baya wasu na kusa da shugaban ne suka shiga tsakani don dakatar batun nada Ogbeh sakataren gwamnatin tarayya.
A cewarsa, sun kirkiri labarin cewa banki na bin Ogbeh bashin kusan biliyan 1 zuwa 2 saboda harkokin noman da yake yi.
A cewar El-Rufa’i, wannan labarin ya sa Buhari ya fasa nada shi, inda daga baya ya sanar da shi cewa wasu abubuwa sun taso kuma ya zaɓi wani daban.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan ya ce ya yi magana da Buhari ya tunasar da shi cewa bashin kudi ba laifi ba ne, domin duk mai harkar noma ko kasuwanci zai iya karɓar bashi.
Leadership ta rahoto cewa ya bayyana cewa wannan labari bai taba fitowa fili ba sai a yanzu da ya yanke shawarar bayyana shi.
El-Rufa'i ya rokawa Ogbeh aljanna
El-Rufa'i ya ce zai ci gaba da yi wa Ogbeh addu’ar samun Aljanna Firdausi duk da bambancin addini, domin ya cancanci hakan bisa irin ayyukan alheri da ya yi.
Daga cikin alherin da Ogbeh ya yi wa kasa, El-Rufa'i ya ce a lokacinsa ne aka daina shigo da shinkafa daga waje saboda habakar noma.
'Dan siyasar ya tuno alheran marigayin yana mai magana kamar ya yi kuka.
Gargadin El-Rufa'i kan zaben Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi gargadi game da zaben Bola Tinubu a 2027.
Ya yi ikirarin cewa idan Tinubu ya samu tazarce a 2027 zai zauna a kan mulki har ya mutu, kamar shugaban Kamaru, Paul Biya.
A kan haka, Nasir El-Rufa'i ya yi kira na musamman ga 'yan Najeriya da su fito fili su kayar da Bola Tinubu a zabe mai zuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


