Nigeria @65: Za a Fara Shagulgulan Ranar 'Yancin kai Ta 2025 a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana taken bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ƴancin kai a shekarar 2025
- Sanarwar ta ce taken ya jaddada muhimmancin haɗin kai, kishin ƙasa da haɗa karfi da karfe domin ci gaban kasa
- Za a gudanar da addu’o’i, taron manema labarai da shirye-shirye daga watan Satumba har zuwa Oktoban 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta fitar da taken bikin ƴancin kai na shekarar 2025, wanda zai mayar da hankali kan hadin kai.
Taken, kamar yadda aka bayyana, na nufin jaddada haɗin kai da haɗa ƙarfi da ƙarfe a tsakanin ’yan kasa domin samar da ci gaba mai ɗorewa.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta fito ne daga daraktan labarai da hulɗa da jama’a na ofishin shugaban ƙasa, Segun Imohiosen, a ranar Laraba a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taken ranar 'yancin kan Najeriya na 2025
A cewar Imohiosen, taken na bana ya mayar da hankali ne kan haɗa dukkan ɓangarorin ƙasa don tabbatar da zaman lafiya.
BBC Hausa ta wallafa cewa ya bayyana cewa ana so al’umma su ɗauki kishin ƙasa a matsayin ginshiƙi wajen ciyar da Najeriya gaba.
A cewarsa, taken ranar 'yancin ya yi daidai da manufar Renewed Hope Agenda ta gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shirin da ake yi kafin ranar 'yanci
Gwamnati ta bayyana cewa za a fara bukukuwa da addu’o’i a masallatai da coci-coci daga ranar 26, Satumba, 2025.
Za a gudanar da addu'o'i a lokacin sallar Juma'a da karfe 1:00 na rana, yayin da za a gudanar da hidimar coci a ranar Lahadi, 28, Satumba, 2025 da karfe 10:00 na safe.
Haka zalika, a ranar Litinin, 29, Satumba, 2025, za a shirya taron manema labarai na duniya domin bayyana shirye-shiryen gwamnati game da zagayowar ranar ƴancin kai.

Source: UGC
Muhimmancin bikin ƴancin kai ga ƙasa
Ranar ƴancin kai, wadda ake gudanarwa duk shekara a ranar 1 ga Oktoba, na tuna wa al’umma tarihi da darasin samun 'yancin kai daga mulkin mallaka na Burtaniya a 1960.
Ana gudanar da bukukuwan da suka haɗa da tarukan fadar shugaban ƙasa, gwamnatocin jihohi, liyafa, da faretin soja.
An sa ran shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabi ga ’yan Najeriya baki ɗaya a ranar bikin, yayin da gwamnoni za su jagoranci bukukuwa a jihohinsu domin nuna kishin ƙasa.
Imohiosen ya kara da cewa duk shirye-shiryen an tsara su ne domin isar da sako na haɗin kai ga dukkan sassa na ƙasa.
Za a fara karatu kyauta a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin karatu kyauta domin inganta kimiya da fasaha a fadin kasar.
Ministan ilimi na tarayya, Dr Tunji Alausa ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya za ta biya kudin makaranta ga sauran daliban makarantun FTC.
Dr Alausa ya bayyana cewa shirin tallafin karatun ya dace da manufar gwamnatin Tinubu ta kawo sauki a Najeriya da inganta ilimi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


