Abin Mamaki: Tsohon Sanata Ya Koma Kauyensu, Ya Karbi Sarautar Magajin Gari
- Gwamna Umo Eno ya nada tsohon Sanatan Akwa Ibom ta Kudu, Nelson Effiong a matsayin Magajin Gari a kauyen Eyo Usotai
- Eno ya mika takardar wannan nadi ga tsohon sanatan da wasu sarakuna daban-daban a wani bangaren bikin cikar Akwa Ibom sbekara 38
- Sanata Effiong ya bayyana cewa ya bar sha'anin siyasa, ya koma fannin sarauta domin taimaka wa al'ummar kauyensu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Tsohon sanata daga Jihar Akwa Ibom, Nelson Effiong, ya zama Magajin Gari na kauyen Eyo Usotai da ke ƙaramar hukumar Oron a jihar.
Sanata Effiong na daya daga cikin sababbin sarakunan gargajiya da suka karɓi takardar nadi daga hannun Gwamna Umo Eno, a ranar Talata, 23 ga Satumba, a Uyo.

Source: Facebook
Gwamna Eno ya tabbatar da nada sarakunan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa hakan wani ɓangare ne na shagulgulan bikin cika shekaru 38 da ƙirƙirar jihar Akwa Ibom a Najeriya.
Gwamna Eno ya nada sababbin sarakuna
A wajen taron, Gwamna Eno ya rantsar da Saviour Udofia, Sarkin Masarautar Abak, a matsayin sabon Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Akwa Ibom.
Gwamnan ya yi amfani da taron wajen jaddada aniyar gwamnatinsa na kula da walwala jin daɗin sarakunan gargajiya.
“Mun samar da motoci na aiki ga sarakuna. Mun canza maku tsofaffin motocin da ku ka dade kuna amfani da su. Za mu ci gaba da kula da lafiyarku," in ji shi.
Ya kuma sanar da ƙarin albashi ga sarakunan gargajiya na jihar tare da naɗa makaɗa na musamman ga kowanne Sarkin masarauta.
Dalilin Sanata Effiong na zama Dagacin kauye
A ranar Laraba, jaridar Premium Times ta tuntubi Effiong kan dalilin da ya sa ya amince ya zama Magajin Gari a kauyensu, inda ya ce:
“Na kammala tafiyar siyasa; yanzu na rumgumi tafiyar gargajiya. Lokaci ya yi da za mu bar wa matasa siyasa. Zan cika shekara 73 a watan Afrilu mai zuwa, da ni ma’aikaci ne da tuni na yi ritaya.”
Effiong ya ce zai maida hankali ne wajen gina zaman lafiya da dorewarta a tsakanin mutanensa da kuma jawo hankalin gwamnati wajen bukatun raya ƙauyen.

Source: Facebook
“Duk da mun yi iya ƙoƙarinmu a siyasa, kowa ya san tasirin da Sarkin kauye, Sarkin kabilu da Sarkin masarauta ke da shi,” in ji shi.
Effiong, wanda aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya wakilci Akwa Ibom ta Kudu a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019, kafin ya sauya sheƙa zuwa APC a shekarar 2017.
Sarkin Ile-Ife ya nada karin sarakuna 20
A wani labarin, kun ji cewa Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya nada sababbin sarakuna 20 a fadar Oodua da ke Ile-Ife a jihar Osun.
Sarkin, wanda ake kira da Ooni na Ile-Ife ya bukaci sarakunan su kasance jagorori na zaman lafiya, hadin kai tsakanin al'umma, tare da samar da ci gaba a yankunansu.
Mai magana da yawun fadar Oodua, Otunba Moses Olafare, ne ya fitar da sanarwar nadin sarakunan, da kuma sunayen wadanda aka nada.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

