Shugaban EFCC Ya Yi Karatun Ta Natsu kan Matsalar Yaki da Cin Hanci
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta shirya wani taron karawa juna sani a babban birnin tarayya Abuja
- Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya yi tsokaci kan muhimmancin hadin kai don yakar masu aikata laifuffuka
- Ola Olukoyede ya nuna cewa hukumar ta dauki hadin kai tsakaninta da masu ruwa da tsaki da matukar muhinmancin gaske
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta tabo batun yakar masu aikata laifuffuka.
Hukumar EFCC ta jaddada kiran haɗin kai da fahimtar juna tsakanin ɓangarori daban-daban domin yaki da laifuffukan tattalin arziki da sauran ayyukan cin hanci a Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana haka a babban ofishin EFCC da ke Abuja yayin wani taron karawa juna sani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ola Olukoyode ya yi jawabi a taron EFCC
Ola Olukoyede, wanda mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya wakilta, ya ce hukumar na ganin kimar haɗin kai da muhimmancin gina fahimtar juna da dukkan masu ruwa da tsaki.
Shugaban na hukumar EFCC ya nuna muhimmancin hadin kai da fahimtar juna wajen samun nasara mai ɗorewa a yakin da ake yi da laifuffukan tattalin arziki da sauran ayyukan cin hanci a Najeriya.
"Ba shakka kafafen yada labarai da kungiyoyin fararen hula suna da matuƙar muhimmanci wajen yaki da dukkan nau’ukan laifuffukan tattalin arziki da sauran ayyukan rashawa."
"Dangantakar tsakanin su kamar kunnen dama da na hagu ne a kan doki guda, domin suna da manufa ɗaya, tona asirin rashin gaskiya da rashin daidai a tsakanin mutane da kungiyoyi a faɗin ƙasa."
"Saboda haka ne hukumar ta ga dacewar kawo su wuri ɗaya a wannan taron karawa juna sanin."
- Ola Olukoyede
An jawo hankalin mahalarta taron EFCC
Wani jami'in hukumar EFCC mai aiki a sashen yaki da laifuffukan intanet, Sam Agbi Enahoro, ya yi magana kan yaudara ta hanyar kuɗin Kirifto da sauran sababbin nau’ukan laifuffukan kuɗi.

Source: Twitter
Jami'in ya gargadi mahalarta taron da su guji shiga kowanne irin kasuwanci ko harkar yanar gizo da zai iya lalata mutuncinsu ko aikinsu.
Ya yi karin bayani kan dabarun da ake amfani da su wajen mu’amalar kuɗin Kirifto tare da jaddada yadda masu zamba ke kara shiga cikin harkar don cutar da jama’a.
An shigar da korafin Kansila gaban EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta samu korafi kan wani Kansila a jihar Katsina.
An shigar da korafin Kansilan ne na mazabar Doro a karamar hukumar Bindawa bisa zargin cin zarafin Naira a wajen wani taron biki da aka gudanar.

Kara karanta wannan
Abin da ka shuka: An yanke wa wasu manyan Sojojin Najeriya 3 hukuncin daurin rai da rai
Mutumin da ya shigar da korafin ya bukaci hukumar EFCC da ta binciki Kansilan, tare da gurfanar da shi gaban kotu idan har an same shi da laifi, don hakan ya zama darasi ga sauran jami'an gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

