Gwamnatin Kano Za Ta Dauki Mataki kan Malamin da Ake Zargi da Taba Mutuncin Manzon Allah SAW
- Wasu gungun matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kano kan zargin da suke yi wa Sheikh Lawal Triumph na batanci ga Annabi SAW
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hadu da masu zanga-zangar yayin da suka isa gidan gwamnatinsa da ke Kano yau Laraba
- Ya bukaci su rubuto korafinsu kan malamin a hukumance, yana mai cewa za a dauki matakin da bai saba wa shari'a ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano bayyana cewa za ta iya daukar matakim shari'a kan fitaccen malamin addinin musulunci nan, Sheikh Lawal Abubakar Triumph.
Gwamnatin ta ce da za ta dauki wannan mataki ne kan zarge-zargen da ake masa na amfani da kalamai masu muni kan fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW a karatunsa.

Source: Twitter
Freedom Radio ta tattaro cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka ga matasan da suka yi zanga-zangar lumana kan zargin da ake wa malamin
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ya bukaci masu zanga-zangar su rubuto korafinsu a hukumance, su aiko masa ta hannun Sakataren Gwamnatin Kano domin da shi za a yi amfani har kotun koli.
Zanga-zanga ta barke kan Sheikh Triumph
Rahotanni sun nuna cewa matasan sun gudanar da wata zanga-zangar lumana da tare da kawo ƙorafi a fadar gidan gwamnatin Kano.
Wannan dai na zuwa ne yayin da wasu 'yan Kano musamman mabiya darikar Tijjaniyya ke zargin cewa Sheikh Triumph na amfani da kalaman da ke taba mutuncin Manzon Allah.
Wane kalamai malamin ya fada kan Annabi SAW?
A baya-bayan nan, an ji Sheikh Triumph na karyata ruwayoyin da ke cewa an haifi Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah Su tabbata a gare shi) da kaciya.
Babban malamin na Sunnah ya ce haihuwar Annabi da kaciya kamar yadda wasu ke yadawa ba karama ba ce, domin ana iya haihwuar gama garin mutane da kaciya.
Malam Lawal Triumph ya ce karama ita ce abin al'ajabin da Allah Ya bai wa Annaba su kadai, yana mai cewa karamomin Annabi Muhammad suna da yawa, amma batun kaciya ko haihuwarsa da kwalli ba su inganta ba.
Wane mataki gwamnatin Kano za ta dauka?
Da yake jawabi ga masu zanga-zangar neman a dauki mataki kan malamin, Gwamna Abba ya bukaci su rubuto korafinsu, su mika wa gwamnati a hukumance.
Gwamnan ya tabbatarwa masu zanga-zangar cewa gwamnatinsa za ta dauki mataki bisa tanadin doka, bayan sun mika korafi kan malamin.

Source: Facebook
A rahoton BBC Hausa, Gwamna Abba Kabir ya ce:
"Za mu dauki matakin da bai saba wa doka ba In Sha Allah, abin da nake so da ku shi ne, ku koma ku rubuto takardar korafi a hukumance, da ita za mu yi amfani daga nan har kotun koli."
'Yan sanda sun gayyaci Sheikh Triumph
A baya, kun ji cewa Rundunar Yan Sandan Kano ta gayyaci Sheikh Triump kan zargin amfani da kalaman da ke taba mutuncin Annabin Allah.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya gayyaci Sheikh Lawan Triumph tare da fara tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki don hana tayar da rikici.

Kara karanta wannan
Abba Gida-Gida zai rage bashin Ganduje, za a biya karin N5bn ga 'yan fansho a Kano
Rundunar ta ce wannan mataki na da nufin dakile yiwuwar rikici tare da tabbatar da cewa kowa na amfani da ‘yancinsa cikin gaskiya da bin doka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

