Majalisa Ta Ballo Ruwa, Tinubu Ya Kira Tsohon Shugaban Rikon Ribas da Minista zuwa Aso Rock
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da tsohon shugaban riko na jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya)
- Wannan ganawa na zuwa ne kwanaki kadan bayan Majalisar Dokokin Ribas ta sha alwashin bincikar mulkin Ibaas na watanni shida
- Ministan Kudi, Wale Edun da shugaban hukumar EFCC na cikin wadanda suka halarci wannan ganawa a fadar shugaban kasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kira tsohon shugaban riko na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), zuwa Fadar Aso Rock da ke Abuja.
Shugaba Tinubu ya gayyaci Ibas, wanda ya rike gwamnatin Ribas na tsawon watanni shida, a daidai lokacin da Majalisar Dokokin jihar ta sha alwashin bincikarsa.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Ibas ya isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 5:50 na yammacin yau Laraba, cikin kayan gargajiya masu ruwan kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya shiga ganawa da Ibas a Aso Rock
Tsohon shugaban rikon ya shiga Aso Rock tare da Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Kasa, Wale Edun, da Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukayede.
Tun da farko, Wale Edun ya shiga fadar shugaban kasa, sai kuma aka ga ya fito cikin gaggawa, kafin daga baya ya dawo dauke da fayil a hannu, abin da ya nuna cewa ganawar na da muhimmanci.
Ibas ya shafe watanni shida yana rike da jihar mai arzikin man fetur a matsayin mai rikon gwamna na wucin gadi.
Ya bar ofis a ranar 17 ga Satumba 2025, bayan karewar wa’adin dokar ta-baci da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanya.
Majalisar Dokokin Ribas ta taso Ibas a gaba
Wannan ya biyo bayan umarnin Tinubu na dawo da gwamnan da ya dakatar, Sir Sim Fubara, mataimakiyaraa da kuma ‘yan majalisar jihar kan kujerunsu daga ranar Alhamis da ta gabata.
A zamanta na farko bayan komawa bakin aiki, Majalisar Dokokin Ribas ƙarƙashin Martin Amaewhule, ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan yadda aka kashe kuɗin jihar a cikin watanni shida da suka gabata.
Sai dai Ibas ya ki amincewa da wannan matakin na binciken kudin da aka kashe a lokacin mulkinsa na wucin gadi, cewar rahoton TVC News.

Source: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa Jihar Ribas ta samu akalla Naira biliyan 254.37 daga Tarayya tsakanin watan Maris da Agusta 2025, a lokacin da Ibas yake rike da mulki.
Ana ganin wannan yunkuri na Majalisar Dokokin Ribas na daya daga cikin dalilan Tinubu na kiran Ibas, Wale Edun da shugaban EFCC domin tattaunawa.
Tinubu ya karbi bakuncin Gwamna Fubara
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Simi Fubara ya kai ziyara ta musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja.
Wannan shi ne karo na farko da Gwamna Fubara ya kai ziyara a fadar Aso Rock Villa tun bayan dawo da shi a matsayin gwamnan jihar Ribas a makon jiya.
Gwamna Fubara ya bayyana godiya marar iyaka ga Shugaba Tinubu bisa shiga tsakanin da ya yi a tare da warware cikin rikicin siyasar jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

