Davido: Shahararren Mawaki Ya Gwangwaje Matarsa da Motar Kusan N300m

Davido: Shahararren Mawaki Ya Gwangwaje Matarsa da Motar Kusan N300m

  • Chioma Adeleke wadda take a matsayin matar shahararren mawaki, David Adeleke, ta samu kyautar mota ta alfarma
  • Shahararren mawakin wanda aka fi sani da Davido ya gwangwaje Chioma da mota ta fadawa duniya wadda ake yayi
  • Davido ya bayyana cewa sai da ya sayar da tsohuwar motarsa tare da kara wasu kudin don yi wa Chioma wannan gagarumar kyautar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Shahararren mawakin Afrobeats na Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi wa matarsa Chioma Adeleke kyauta mai tsoka.

Davido ya yi wa Chioma kyautar sabuwar mota kirar Mercedes-Benz G-Wagon 2025.

Davido ya yi wa Chioma kyautar mota
Hoton David Adeleke da matarsa Chioma Adeleke @davido
Source: Instagram

A wani bidiyo da Davido ya wallafa a Instagram Story dinsa a ranar Laraba, an gan shi cikin farin ciki yayin da yake karɓar motar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Motar G-Wagon ta faso kasuwa

Kara karanta wannan

Trump ya ce an masa makarkashiya bayan ya samu matsaloli 3 a taron UN

Motar ta alfarma, wadda aka fara fitarwa a kasuwa cikin 'yan kwanakin nan, tana da farashin sama da $150,000 (Naira miliyan 240).

Sabon samfurin motar na 2025 na ɗauke da kira ta zamani, ciki har da zaɓin amfani da wutar lantarki, abin da ya sa ta bambanta da na baya.

Davido ya yi wa Chioma kyautar mota

A cikin bidiyon ya bayyana yadda ya sayar da tsohuwar G-Wagon ɗinsa sannan ya kara kuɗi don sayo sabuwa.

“Da farko sai da muka cire wadda na saya a baya, sannan na kara kuɗi domin samun wannan sabuwar.”

Davido ya bayyana cewa dalilin yin hakan shi ne nuna ƙaunar da yake yi wa matarsa, inda ya jaddada cewa:

"Abu mafi kyau kawai zan iya ba matata.”

Lokacin da ya mika motar ga Chioma, ta nuna farin ciki sosai, yayin da Davido ke murna yana cewa:

"Mun yi a 2025!”
Davido ya yi wa Chioma kyautar motar N250m
Hoton Davido tare da Chioma da motar G-Wagon 2025 da ya saya mata Hoto: @thehefchi
Source: Instagram

Auren Davido da Chioma ya dauki hankali

A baya-bayan nan, auren Davido da Chioma Adeleke ya kasance babban abin magana, inda aka yi jerin biki uku masu kayatarwa.

Kara karanta wannan

Ewugu: Tsohon mataimakin gwamnan da 'yan bindiga suka sace kafin ya rasu

Na karshe shi ne auren coci da aka gudanar a birnin Miami ranar 10 ga watan Agusta, 2025.

Wannan biki ya biyo bayan auren kotu da aka yi a watan Maris 2023, da kuma auren gargajiya da aka gudanar a Legas a watan Yunin 2024.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa auren farin kaya da aka gudanar a Miami ya lashe kuɗi har Dala miliyan 3.7.

Manyan mutane da suka hada da attajirai, ’yan siyasa, da fitattun ’yan wasa da ’yan fim daga Najeriya da kasashen waje sun samu halartar bikin.

Davido ya samu kyautar mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, ya samu kyautar dankareriyar mota.

Davido ya samu kyautar dankareriyar mota kirar Cadillac Escalade 600 daga wani kamfanin sayar da ababen hawa wanda yake da hedikwata a birnin Dallas na jihar Texas.

Kamfanin sayar da ababen hawan dai ya yi kyautar motar ne ga Davido domin taya shi murnar cika shekara 32 da haihuwa a duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng