Sarki Sanusi II Ya Hadu da Ministocin Tinubu a Majalisar Dinkin Duniya

Sarki Sanusi II Ya Hadu da Ministocin Tinubu a Majalisar Dinkin Duniya

  • Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya gabatar da jawabi a taron Goalkeepers 2025 a birnin New York kan kare rayuwar yara
  • Sarkin ya gana da Bill Gates da Fasto Rick Warren inda suka tattauna dabarun ci gaba mai dorewa a Kano da Najeriya
  • Sanusi II ya halarci taron Afrika a majalisar dinkin duniya, tare da ganawa da Sarauniya Máxima game da hada-hadar kudi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Khalifa Dr Muhammadu Sanusi II, ya gudanar da muhimman ayyuka bayan halartar taruka a birnin New York, Amurka.

Mai martaban ya wakilci jihar Kano a manyan tattaunawa kan ci gaban al’umma da hadin kai na duniya.

Sanusi II, Yusuf Tuggar da Muhammad Badaru Abubakar
Sanusi II, Yusuf Tuggar da Muhammad Badaru Abubakar. Hoto: Sanusi Dynasty II
Source: Facebook

Masarautar Kano ta wallafa a X cewa Sanusi II ya halarci taron 'yan Afrika da aka shirya a gefen babban zauren Majalisar Dinkin Duniya yayin da ake taron UN karo na 80.

Kara karanta wannan

Hotunan manya a Najeriya da suka halarci bikin karrama Rarara da digirin Dakta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wajen taron, ya gana da Sarauniya Máxima ta Netherlands inda suka tattauna batutuwan shigar da mata da matasa harkokin ilimi da hada-hadar kudi.

Jawabin Muhammadu Sanusi II a taro a Amurka

A ranar Litinin, 22 ga Satumba, 2025 Sarkin ya gabatar da muhimmin jawabi a taron Goalkeepers na 2025

Rahotanni sun nuna cewa shirin yana karkashin kulawar cibiyar Bill da Melinda Gates kuma ya mayar da hankali ne kan yaki da mutuwar yara da za a iya kauce wa.

Sanusi II ya yi kira da a dauki matakai masu dorewa domin kare lafiyar yara da inganta kiwon lafiya a nahiyar Afirka, tare da jaddada rawar da al’umma da shugabanni ke takawa.

Sarki Sanusi II ya gana da Bill Gates

Har ila yau, Sanusi II ya halarci taro a cibiyar Bill da Melinda Gates, inda ya gana da Bill Gates da Fasto Rick Warren.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Malamin da ya fi 'tsufa' yana wa'azi ya bar duniya yana shekaru 95

Rahotanni sun bayyana cewa tattaunawar ta fi karkata kan dabarun ci gaba mai dorewa musamman a jihar Kano.

Sanusi II na tattaunawa da Bill Gates a Amurka
Sanusi II na tattaunawa da Bill Gates a Amurka. Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Facebook

An yi nazari kan yadda za a inganta kiwon lafiya, ilimi, da tattalin arzikin kananan hukumomi a jihar, tare da kawo hanyoyin saka jari da tallafawa shirye-shiryen ci gaban al’umma.

Sanusi II ya je majalisar dinkin duniya

A ranar Talata, 23 ga Satumba, 2025, ya halarci wani taro a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya tare da Ministocin Harkokin Waje da na Tsaron Najeriya, Yusuf Tuggar da Muhammad Badaru

Haka kuma, Sarkin Ban Kano, Dr Mansur Muhtar Adnan, ya kasance tare da shi a wannan ziyara mai tarihi.

A cikin wannan tafiya, Sanusi ya je cibiyar Majalisar Dinkin Duniya tare da manyan mutane, ciki har da Sarkin Fulanin Gombe, Alhaji Umaru Kwairanga.

Mai martaba Sanusi II ya gama PhD

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya kammala karatun digirin PhD a jami'ar London.

Rahotanni sun bayyana cewa Sarkin ya shiga makarantar ne bayan sauke shi da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Filato da ake nema ruwa a jallo ya mika kansa, ICPC ta tsare shi

Legit Hausa ta gano cewa manyan mutane daga jihar Kano sun halarci bikin gama karatun, ciki har da gwamna Abba Kabir Yusuf.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng