An Cinnowa Jami'an Gwamnati EFCC kan Zargin Cin Zarafin Naira
- Matsala ta tunkaro wani Kansila a karamar hukumar Bindawa ta jiha Katsina bayan an shigar da korafi a kansa a gaban hukumar EFCC
- An shigar da korafin ne bisa zargin Kansilan da cin zarafin kudin Naira wanda hakan ya sabawa doka
- Hukumar EFCC ta sha gurfanar da mutane a gaban kotu kan zargin cin zarafin Naira, inda wasu har kulle su ake yi a gidan gyaran hali
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - An shigar da korafi a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), kan wani Kansila a jihar Katsina.
Hukumar EFCC ta samu korafin ne kan zargin karya dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kansilan Mazabar Doro, a karamar hukumar Bindawa, jihar Katsina, ya aikata.

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa wani Dr. Sani Ahmad daga Abuja ya sanya hannu kan korafin da aka mika gaban hukumar EFCC.

Kara karanta wannan
Ta'addanci: Shugaban Nijar, Tchiani ya fito da sababbin zarge zarge a kan Faransa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An hada Kansila da hukumar EFCC
Dr. Sani Ahmad ya zargi Kansilan da watsawa da lalata takardun kuɗin Naira a lokacin wani taron biki kwanan nan.
A cewar Dr. Sani Ahmad, Kansilan ya aikata hakan a fili, a gaban jama’a tare da shaidu da kuma bidiyon da aka ɗauka a wurin bikin, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar da labarin.
Ya yi nuni da sashe na 21 na dokar CBN, 2007, inda aka fayyace cewa duk wani cin zarafin kuɗin kasa babban laifi ne.
Dokar ta hana watsawa, lalatawa ko cin zarafin Naira, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci tarar akalla N50,000 ko zaman gidan yari na watanni shida, ko duka biyun.
"Kansilan, wanda a matsayinsa na jami’in gwamnati ake tsammanin ya zama abin koyi, ya karya wannan doka ta hanyar watsawa da lalata Naira."
"Wannan abin da ya yi, ya aika sako mara kyau ga matasa, tare da rage darajar kuɗin kasarmu."
- Dr. Sani Ahmad
Wace bukata aka nema wajen EFCC?
Dr. Sani Ahmad ya bukaci EFCC ta binciki lamarin, ta gurfanar da Kansilan a gaban kotu idan an same shi da laifi.

Source: UGC
Ya kuma bukaci hukumar ta yi amfani da lamarin a matsayin gargadi ga sauran jami’an gwamnati kan muhimmancin mutunta dokokin kuɗi na kasa.
Hakazalika ya kara bayyana shirinsa na yin aiki tare da masu bincike, inda ya jaddada cewa korafin an gabatar da shi ne cikin gaskiya domin kare mutuncin tsarin shari’a na Najeriya da kuma kiyaye darajar kuɗin Naira.
EFCC ta gurfanar da tsohon minista gaban kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), ta sake gurfanar da tsohon ministan lantarki, Dr. Olu Ogunloye, a gaban kotu.
Hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon ministan ne a gaban kotu bisa zargin aikata laifuffuka bakwai da suka shafi karɓar rashawa da bijire wa umarnin shugaban kasa.
Tsohon ministan wanda aka gurfanar a gaban mai shari’a Jude Onwuegbuzie, inda ya karyata dukkan zarge-zargen da aka karanto masa a gaban kotu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

