Gwamnatin Abba Ta 'Daura 'Damarar Yaki da Daba, Ta Dauki Matasa 600 Aiki a Kano

Gwamnatin Abba Ta 'Daura 'Damarar Yaki da Daba, Ta Dauki Matasa 600 Aiki a Kano

  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fara horas da matasa 380 cikin sahun farko na masu aiki na musamman na yaki da kwacen waya a Kano
  • An fara horon ne a makarantar tsaro ta jihar da ke Gabasawa na tsawon makonni biyu domin ba su kwarewar aikin tsaro yadda ya kamata
  • Za a ba wa masu horon albashi na wata-wata bayan kammala shirin, kuma za su taimaka wajen samar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoGwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da horas da sahun farko na matasa 380 daga cikin 600 da aka dauka don aikin musamman na yaki da satar waya.

Haka kuma ana sa ran matasan za su kare lafiyar manyan baki (VIPs), a wani bangare na sabunta kokarin da ake yi don yaki da 'yan daba da sauran laifuffuka a fadin jihar.

Kara karanta wannan

'A ina 'yan bindiga ke samun makami?' An yi wa Tinubu tambaya mai zafi

Gwamnatin Kano ta dauki matasa aiki
Hoton Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa ana gudanar da horon na tsawon makonni biyu a makarantar koyon tsaro ta Jihar Kano da ke Gabasawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kano na horas da matasa

Daily Post ta ruwaito cewa gwamnatin Kano ta ce an dauki matasan aiki ne da nufin ba su kwarewar da ta dace don kare rayuka da dukiyoyi a jihar.

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a da Wayar da Kai na Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Musamman ta Jihar Kano, Muhammad Idris, ya fitar.

Ya bayyana cewa matasan da ake bai wa horo a yanzu sun fito ne daga cikin matasa 600 da aka dauka domin aikin.

Ya ce:

“Horon na da nufin koyar da matasa dabaru da tarbiyyar da suka dace don su taimaka wa hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da doka a fadin jihar."

Wadanda za su horar da matasa a Kano

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida zai rage bashin Ganduje, za a biya karin N5bn ga 'yan fansho a Kano

Kwamandan Makarantar Tsaro ta Jihar Kano da ke Gabasawa, Kyaftin Muhammad Bello Mai Gaskiya mai ritaya shi ne ya tarbi matasan da za a horas a wannan bangare.

Ya bayyana cewa shirin yana da nufin koyar da matasan dabarun yaki da miyagun laifuffuka da suka zama ruwan dare a Kano, musamman satar waya da tayar da tarzoma a birnin Kano.

Tsojon sojan ya ce horon zai mayar da hankali ne kan hana satar waya, kare lafiyar manyan baki da dabarun tuki cikin nutsuwa.

Za a horas da matasan Kano a kan tsaro
Hoton Injiniya Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Haka kuma matasan za su dauki darussa daga hukumar NDLEA, shawarwari daga jami’an Hisbah, atisayen motsa jiki da kuma yin gwaje-gwaje.

Mai Gaskiya ya bukaci mahalarta horaswar da su jajirce wajen cimma manufofin shirin, ya ce rawar da za su taka za ta taimaka matuka wajen dawo da zaman lafiya a unguwannin Kano.

Wasu daga cikin mahalarta horon sun bayyana godiyarsu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da alkawarin yin aiki da gaskiya da rikon amana.

Fursunoni sun ci jarrabawar NECO a Kano

A wani labarin, mun wallafa cewa Hukumar kula da fursunoni ta Najeriya, ta ce wasu daga cikin daurarru a Kano sun yi nasara sosai a jarrabawar kammala sakandare ta NECO.

Kara karanta wannan

Sakkwato: Shugabannin makarantun sakandare 6 sun tsunduma kansu a matsala

A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin, fursunoni 68 ne suka ci gaba da yin fice a wannan jarabawa, lamarin da ya sanya farin ciki a zukatan wadanda abin ya shafa.

Wasu daga cikin fursunonin da suka zauna jarabawar sun bayyana godiya da jin dadinsu kan wannan dama da suka samu, wanda ke nuna lamar cewa rayuwa za ta iya yin kyau a gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng