Malami: DSS Ta Titsiye Tsohon Ministan Buhari kan Harin 'Yan Daba

Malami: DSS Ta Titsiye Tsohon Ministan Buhari kan Harin 'Yan Daba

  • Tsohon ministan shari'a a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Abubakar Malami, ya amsa gayyatar hukumar DSS
  • Abubakar Malami ya bayyana cewa jami'an na hukumar DSS sun yi masa tambayoyi kan binciken da su ke yi
  • Tsohon ministan ya yaba kan yadda ganawarsa da jami'an na DSS ta kasance cikin karramawa da mutunta juna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Hukumar tsaro ta DSS ta yi wa tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami SAN tambayoyi.

Hukumar DSS ta yi tambayoyi ga Abubakar Malami ne kan harin da aka kai wa jerin gwanon motocinsa a jihar Kebbi.

Abubakar Malami ya amsa gayyatar DSS
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Twitter

Tsohon ministan ya tabbatar da hakan ne a shafinsa na Facebook ranar Litinin, 22 ga watan Satumban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi tambayoyin ne a ofishin hukumar DSS na Birnin Kebbi, inda Malami ya bayyana cewa an gudanar da binciken cikin kwarewa da mutuntawa.

Kara karanta wannan

Matsala ta girma: An gano gawarwakin yan sanda 8 bayan sun bace a Najeriya

'Yan daba sun farmaki tawagar Malami

Idan ba a manta ba a ranar 1 ga watan Satumba, 2025, wasu da ake zargin ’yan daban siyasa ne sun kai hari kan tawagar Malami a Birnin Kebbi.

Lamarin ya faru ne bayan dawowarsa daga gaisuwar ta’aziyya ga iyalan wani marigayi babban limamin masallacin Juma'a.

A lokacin harin, an lalata motoci kusan 10 da ke cikin tawagar, yayin da dama daga cikin magoya bayansa suka samu raunuka.

Tsohon ministan, wanda shi ne jagoran jam’iyyar ADC a jihar Kebbi, ya bayyana harin a matsayin wanda ya samo asali daga “dalilan siyasa”.

Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta nesanta kanta daga lamarin, amma daga bisani Malami ya shigar da korafi ga hukumomin tsaro ciki har da ’yan sanda da DSS.

Yadda ta kaya tsakanin Malami da DSS

A bayanin da ya yi a daren Litinin, Malami ya ce an yi masa tambayoyi cikin mutuntawa, inda ya jaddada cewa zai ci gaba da hada kai da DSS don tabbatar da an gudanar da bincike yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027

Malami ya sha tambayoyi a hannun DSS
Hoton tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Facebook
"Zan iya tabbatar da cewa hukumar DSS ta gayyace ni don taimakawa bincike kan harin da aka kai min da tawagata a jihar Kebbi ranar 1 ga Satumba, 2025."
"Ƙorafin da aka shigar na da alaka da manyan ’yan siyasar adawa a jihar. Ina yabawa DSS bisa yadda suka gudanar da bincikensu cikin kwarewa da gaskiya."
"An mutunta ni cikin girmamawa, kuma ina nan a shirye kan ci gaba da bayar da haɗin kai domin tabbatar da an kammala binciken cikin nasara."

- Abubakar Malami

Gwamnan Kebbi ya zargi Malami

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris Kaursn Gwandu, ya yi zarge-zarge kan tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami.

Gwamna Nasir ya zargi Malami da daukar siyasa tamkar hanyar yada ayyukan ta'addanci biyo bayan koken da ya rubuta ga hukumomin tsaro.

Hakazalika, gwamnan ya bayyana cewa kalaman tsohon ministan sun sanya tsoro.a zukatan masu zuba hannun jari daga kasashen waje wadanda ke shirin kafa masana'antu a Kebbi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng