Fursunoni a Kano Sun Yi Jarrabawar NECO, kusan Mutum 70 Sun Yi Zarra

Fursunoni a Kano Sun Yi Jarrabawar NECO, kusan Mutum 70 Sun Yi Zarra

  • Fursunoni akalla 68 a jihar Kano na daga cikin daliban da su ka ci jarabawar kammala sakandare ta NECO a shekarar 2025
  • Wannan al'amari na zuwa a lokacin da gwamnati da sauran jama'a ke murnar ƙoƙarin daliban da jihar su ka yi a bana
  • Hukumar kula da gyaran hali ta reshen Kano ta ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ne ya ɗauki nauyin karatun dalibai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar kula da fursunoni ta Najeriya, reshen Jihar Kano, ta bayyana cewa wasu daga cikin daurarrua Kano sun yi fice a NECO.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Litinin, ta ce fursunoni 68 sun yi nasara a jarabawar kammala sakandare ta NECO a bana.

Kara karanta wannan

Abin kunya: An kama masu karkatar da kudin tallafin 'taki' da ake rabawa talakawa a Katsina

Fursunonin Kano sun ci jarrabawar NECO
Hoton Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa wannan nasara, a cewar hukumar, ta zama babban abin farin ciki ga waɗanda abin ya shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fursunoni a Kano sun ci jarrabawar NECO

Daily Post ta wallafa cewa wasu daga cikin fursunonin sun bayyana cewa wannan dama ce ta musamman da za ta taimaka musu wajen sake gina rayuwarsu.

A cewar guda daga cikin daliban ta cikin sanarwar:

“Wannan nasara ba ƙaramar abu ba ce a gare mu. Ta ba mu kwarin gwiwa za mu iya sake zama al’umma nagari idan Allah ya ba mu dama mu fito."

Hukumar ta nuna cewa nasarar ba ta zo haka kawai ba, illa dai saboda goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano.

Gwamnatin Kano na taimakon fursunoni

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar Kano ce ta ke ɗaukan nauyin shirye-shiryen ilimantar da su da ake yi wa fursunonin.

A cikin sanarwar, hukumar ta ce wannan shiri na ilimi da horo ya yi daidai da dokar Hukumar Kula da Fursunoni ta shekarar 2019.

Kara karanta wannan

Sakkwato: Shugabannin makarantun sakandare 6 sun tsunduma kansu a matsala

A cewar ta, dokar ta mayar da hankali wajen gyara halaye da kuma ba da sabuwar tarbiyya ta hanyar karatu da koyon sana’o’i.

Gwamnatin Kano ta nanata alkawarin inganta ilimi a Kano
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ta ce gwamnatin Kano ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da ba fursunoni damar koyon ilimi domin su samu mafita bayan sun kammala wa’adin zaman su a gidan yari.

A cewar sanarwar, gwamnati ta ce:

“Mun kuduri aniya cewa za mu samar da hanyoyin karatu da koyon sana’o’i ga fursunoni domin su koma cikin al’umma a matsayin mutanen kirki, wadanda za su ba da gudummawa wajen gina kasa."

Gwamnatin Kano za ta dauki karin malamai

A baya, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta dauki malamai 4,315 don kara wa makarantun jihar karfi.

Wasu daga cikin waɗanda za a dauka aiki, malamai ne da ke koyarwa na wucin gadi a wasu makarantun jihar, yayin da aka dauki wadansu da ke aiki a tsarin BESDA.

Gwamnatin ta ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen inganta harkar ilimi, musamman ganin yadda daliban jihar Kano suka yi fice a jarabawar NECO.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng