Bugaje: Tsohon dan Majalisa Ya 'Karyata' Obasanjo kan Neman Wa'adi na 3
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya musanta batun cewa ya yi kokarin neman wa'adin mulki karo na uku
- Sai dai, Dr. Usman Bugaje ya fito ya bayyana cewa abin da tsohon shugaban kasan ya fadi ba gaskiya ba ne
- Tsohon dan majalisar ya nuna cewa akwai kwararan shaidu da za su tabbatar da cewa Obansanjo, ya nemi ya ci gaba da rike madafun ikon kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon ɗan majalisar wakilai, Dr. Usman Bugaje, ya yi martani kan ikirarin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, na cewa bai nemi tazarce karo na uku ba.
Dr. Usman Bugaje ya jaddada cewa tsohon shugaban kasan ya yi duk mai yiwuwa domin tsawaita zamansa a kan mulki.

Source: Twitter
Dr. Usman Bugaje ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Morning Show' na tashar Arise tv ranar Litinin, 22 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obasanjo ya musanta neman wa'adi na uku
A makon da ya gabata a wani taron tattaunawa kan dimokuraɗiyya da gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a kasar Ghana, Obasanjo ya yi watsi da batun wanda ya daɗe tana jawo cece-kuce.
Obasanjo ya bayyana cewa bai taɓa neman wa’adin mulki na uku ba duk da zargin da ake yi.
Me Bugaje ya ce kan Obasanjo?
Bugaje wanda ya kasance ɗan majalisa a lokacin mulkin Obasanjo, ya dage cewa 'yan majalisu a wancan lokaci suna da masaniya game da shirin neman wa’adin mulki na uku.
“Zan iya tabbatar maka cewa Obasanjo ya nemi wa’adin mulki na uku. Ya yi duk abin da zai iya a karkashin ikonsa domin samun wa’adin mulki na uku, amma ya kasa cimma hakan.”
- Dr. Usman Bugaje
Tsohon ɗan majalisar ya ce hujjar Obasanjo ba ta da karfi, inda kara da cewa wakilan Obasanjo sun yi barazana ga ‘yan majalisa da dama a lokacin.
"Yanzu, kawai saboda bai ɗauki waya ya kira wani kai tsaye ba, ba hujja ba ce cewa bai nemi wa’adin mulki na uku ba."
"Kawai basaja ne amma mu a Majalisar Tarayya a wancan lokacin mun san babu wata shakka cewa ya yi aiki dare da rana don cimma wannan buri, kuma da yawa daga cikinmu mun fuskanci barazana daga wajen wakilansa."
- Dr. Usman Bugaje
Bugaje ya tuna abin da aka yi wa 'yan majalisa
Bugaje ya kuma tuno barazanar da aka yi wa ‘yan majalisa, inda ya kawo misali da Sanata Victor Lar, wanda a wancan lokaci ya kasance shugaban 'yan majalisar wakilai na Arewa.

Source: Twitter
Ya ce an tilasta masa yin ɓuya a lokuta daban-daban kafin taron karshe da aka yi don kaɗa kuri’ar kin yarda da shirin wa’adin mulki na uku.
"Waɗanda suka rarraba kuɗin, waɗanda aka ba su kuɗin, da kuma waɗanda suka ki karɓar kuɗin duk suna raye. Akwai kwakkwaran shaida, wannan magana ba za a iya musanta ta ba. Babu yadda zai yi ya ce bai nema ba."

Kara karanta wannan
Jonathan ya kada hantar shugabanni, ya fadi abij da ya kamata a yi wa marasa katabus
- Dr. Usman Bugaje
Obasanjo ya magantu kan dimokuradiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya koka kan halin da dimokuradiyya take ciki.
Obasanjo ya nuna damuwar cewa tsarin dimokuradiyya na fuskantar barazanar rushewa idan aka ci gaba da tafiya da shi a haka.
Tsohon shugaban kasan ya bayyana cewa dole ne a sake fasalta dimokuradiyya idan har ana son kaucewa mutuwarta gaba daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

