Tsohon Dan Bindiga Mai Shekara 70 da Ya Ajiye Makamai Ya Yi Jawabi a Katsina

Tsohon Dan Bindiga Mai Shekara 70 da Ya Ajiye Makamai Ya Yi Jawabi a Katsina

  • Tsohon shugaban ’yan bindiga mai shekaru 70, Sani Geza ya nuna farin ciki da yarjejeniyar sulhu a yankin jihar Katsina
  • Sanu Geza ya ce shekaru da dama suna fatan samun zaman lafiya tare da barin garkuwa da mutane da ta’addanci
  • Hukumomin tsaro da gwamnatin Katsina na cigaba da amfani da tattaunawa da dabarun soji wajen kawo karshen matsalar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Wani tsohon shugaban ’yan bindiga, mai suna Sani Geza, ya bayyana jin daɗinsa da kuma farin ciki bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya a Matazu, jihar Katsina.

Hakan na zuwa ne bayan sulhu a tsakanin shugabannin al’umma da kungiyoyin da ke dauke da makamai.

Dan bindiga mai shekara 70 da ya tuba a Kastina
Dan bindiga mai shekara 70 da ya tuba a Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa matakin ya zo ne bayan dogon lokaci na rashin kwanciyar hankali da hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban na jihar.

Kara karanta wannan

Katsina: Kananan hukumomi 2 sun zauna da ƴan ta'adda ɗauke da mugayen makamai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Geza da ya shafe shekaru cikin rayuwar yaƙi da tashe-tashen hankula, ya bayyana wannan yarjejeniya a matsayin babbar damar da aka jima ana jira.

Yarjejeniyar sulhun ta jawo hankalin al’umma da dama, musamman mazauna yankin da suka sha fama da hare-haren ’yan bindiga.

Maganar dan bindiga mai shekara 70

Sani Geza na cikin wadanda aka sani da zama daya daga cikin tsofaffin shugabannin kungiyoyin ’yan bindiga a Katsina.

Ya bayyana cewa shi da mabiyansa sun daɗe suna jiran damar da za su bar rayuwar fada su rungumi zaman lafiya.

Geza ya kara da cewa lokaci ya yi da za su mayar da hankali wajen gyaran rayuwarsu da kuma zaman lafiya tsakanin al’umma.

Ya kuma yi addu’a da fatan wannan yarjejeniya ba za ta zama abin wasa ba, sai dai ta dore ta zama hanyar da za ta kawo sauyi mai ma’ana a rayuwar jama’a da kuma mazauna jihar.

Wasu 'yan bindiga da suka halarci zaman sulhu a Katsina
Wasu 'yan bindiga da suka halarci zaman sulhu a Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

Rawar al’umma kan sulhu a Matazu

Kara karanta wannan

Daga Kaduna, Taraba da wasu jihohi ake kai hari a Filato inji rahoton gwamnati

Shugabannin al’umma da suka shiga tattaunawar sun bayyana cewa yarjejeniyar wani bangare ne na shirin kawo zaman lafiya a dukkan sassan Katsina.

Sun bayyana cewa tattaunawa da gina amincewa tsakanin al’umma da masu dauke da makamai na daga cikin hanyoyin da za su tabbatar da dorewar zaman lafiya.

Mazauna yankin sun nuna jin daɗinsu, suna jaddada cewa matakin ya bude sabuwar kafar cigaba, musamman wajen dawo da ayyukan noma da kasuwanci.

Kokarin gwamnati da jami’an tsaro

Gwamnatin Katsina tare da hukumomin tsaro sun kara azama wajen shawo kan matsalar ta’addanci da garkuwa da mutane, inda suka haɗa dabarun soji da na tattaunawa.

Yayin da sojoji ke cigaba da farautar 'yan ta'adda, yankuna da dama na jihar Katsina sun fara sulhu da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.

A ina 'yan ta'adda ke samun makami?

A wani rahoton, kun ji cewa bayyanar 'yan bindiga da ke dauke da manyan makamai a wuraren sulhu na cigaba da jan hankali.

An bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin ganin cewa an dakile hanyar da 'yan ta'adda ke samun makami.

Kara karanta wannan

Jagoran 'yan bindiga ya fara cika alkawari kan yarjejeniyar sulhu a Katsina

Abin da ya fi jan hankali shi ne ganin 'yan ta'adda na zuwa zaman sulhu kuma suna komawa daji da makaman da suka mallaka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng