'A ina 'Yan Bindiga ke Samun Makami?' An Yi wa Tinubu Tambaya Mai Zafi
- Ana yawan kashe daruruwan mutane a Najeriya ta hannun ‘yan fashi, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ke amfani da makamai ba bisa ƙa’ida ba
- Dokar Najeriya ta haramta mallakar bindiga ba tare da lasisi ba, tare da tanadar da hukunci mai tsanani ga wanda aka kama da ita
- Ƴan kasa na kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya umarci jami’an tsaro su kwace makamai daga hannun masu laifi domin kare rayuka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ƴan kasa da dama sun fara bayyana damuwarsu kan yadda ake ci gaba da kashe jama'a a duk fadin ƙasar nan da makamai marasa lasisi.
Tambayar da ake ta yawo da ita, ita ce: daga ina waɗannan miyagu ke samun makaman da suke amfani da su wajen kai hare-hare?

Source: Twitter
Tribune ta wallafa cewa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, sashe na 33(1), ya ce kowane ɗan ƙasa na da hakkin rayuwa, kuma ba za a iya kashe shi da gangan ba sai da hukuncin kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da haka, kisan gilla na kara yawaita musamman a yankin Arewa maso Yamma inda ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar jama’a.
Wasu na ganin lokaci ya yi da shugaban ƙasa Bola Tinubu zai ɗauki mataki mai tsauri wajen ganin cewa an kwace makaman da ke yawo a hannun ‘yan ta’adda da kuma hana shigowarsu.
Tambayar da ake yi wa shugaban ƙasa
Malam Mumin ya rubuta wata wasika inda ya bayyana cewa ana kashe daruruwan ‘yan kasa kullum da irin wadannan makamai.
Ya tambayi gwamnatin tarayya abin da take tsammanin talakan Najeriya zai yi domin kare kansa idan ‘yan fashi suka shiga gidansa da tsakar dare da bindiga.
Ya ce lamarin ya kai ga maharan na kashe masu gadi a gidaje yayin da suke kokarin kare masu gidan da suke aiki. Wannan, a cewarsa, babban ƙalubale ne ga gwamnati da ‘yan sanda.
Bukatar 'yan sanda su dauki mataki
Mumin ya yi kira ga shugaban kasa ya umarci sufeton na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya baza jami’ansa a sassan Najeriya domin kwace makamai marasa lasisi daga hannun ‘yan ta’adda.
Haka zalika ya kuma nemi a cafke wadanda ke shigo da bindigogi ta haramtacciyar hanya zuwa Najeriya.
A cewarsa, idan aka bar wannan matsala ta ci gaba, rayukan miliyoyin ‘yan kasa za su ci gaba da kasancewa cikin haɗari.

Source: Facebook
Ƴan ta’adda na nuna makamai
Mumin ya kuma bayyana damuwa kan yadda aka saba ganin ‘yan bindiga suna zuwa tarukan zaman lafiya a jihohin Arewa maso Yamma.
Mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama, ya yi tsokaci a X kan yadda 'yan ta'adda ke nuna makamai yayin da ake zaman sulhu da su a Katsina.
An kai hari a banki a Anambra
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari wani bankin Polaris a jihar Anambra.
Rahotanni sun bayyana cewa bankin na cigaba da bincike domin gano adadin kudin da aka sace yayin harin.
Rundunar 'yan sanda ta kaddamar da bincike domin gano 'yan ta'addan da suka kai harin yayin da bankin ya fara binciken cikin gida.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


