Abba Gida Gida zai Rage Bashin Ganduje, Za a Biya Karin N5bn ga Ƴan Fansho a Kano

Abba Gida Gida zai Rage Bashin Ganduje, Za a Biya Karin N5bn ga Ƴan Fansho a Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf zai biya ƙarin N5bn ga fansho da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta gaza biya a zamaninta
  • Sanarwar da gwamnati ta fitar a ranar Lahadi ta bayyana cewa wannan na nufin jimillar kudin fanshon gwamnatin baya da aka rage zai kai N27bn
  • Wannan mataki ya zo ne a wani ɓangare na shirin gwamnati na biyan hakkin ma’aikata da iyalan wadanda su ka rasu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano zai ƙaddamar da mataki na biyar na biyan bashin fansho da wadanda su ka rasu a bakin aiki.

Gwamnatin ta sanar da cewa za ta kaddamar da shirin a ranar Laraba, 24 ga Satumba, 2025 domin rage wa tsofaffin ma'aikatan da iyalansu matsin rayuwa.

Kara karanta wannan

Sakkwato: Shugabannin makarantun sakandare 6 sun tsunduma kansu a matsala

Gwamnatin Kano za ta kara biyan yan fansho hakkinsu
Abba Gida Gida yayin da ya ke mika hakkin wani ma'aikacin jihar ga iyalansa Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Sanarwar da hadimin Gwamna, Ibrahim Adam ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi ta bayyana cewa za a raba N5bn ga tsofaffin ma'aikatan da iyalan wadanda su ka rasu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba zai rage bashin fanshon gwamnatin Ganduje

Sanarwar ta kara da bayyana cewa za a bayar da kudin ne ga tsofaffin ma’aikata da su ka kammala aiki a tsakanin shekarun da Ganduje ya yi mulkin Kano.

Mai ba wa Gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam ya ce wannan kari ne a kan N22bn da gwamnatin ta biya a baya.

Ya ce wannan na daga cikin N48bn da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bari a matsayin bashin fansho da hakkokin ma'aikatan da su ka rasu.

Gwamnatin Kano za ta kaddamar da biyan yan fansho a mako mai zuwa
Abba Gida Gida a ranar bikin ma'aikata a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Kudin da gwamnatin ta fitar a baya, wato karo na hudu ta biya N6bn domin biyan biyan tsofaffin ma'aikatan da su ka cancanta.

A lokacin, Gwamnan ya bayyana cewa shirin nasa yana da nufin magance kukan jama'a da su ka amince da zabensa domin ya share masu hawaye.

Kara karanta wannan

Bayan nasarar dalibanta a NECO, gwamnatin kano za ta dauki malamai 2, 600 aiki

Gwamnati: Mun kusa gama biyan 'yan fansho

A cewar Ibrahim Adam, sabon N5bn da za a raba mako mai zuwa zai zama mataki na biyar na biyan bashin fanshon tsofaffin ma'aikatan da su ka hidimta wa kasa.

Ya ƙara da cewa:

“Wannan biyan fansho ba wai kawai yana rage ƙuncin da iyalai da tsofaffin ma’aikata ke ciki ba ne, har ma yana tabbatar da alkawarin gwamnatin Abba share hawayen jama'a da adalci."

Adam ya tabbatar da cewa an riga an biya wani ɓangare na tsofaffin ma’aikatan shekarar 2017 da 2019, kuma cikin mako mai zuwa za a kammala biyan sauran.

Wannan, a cewarsa, zai ƙara sauƙaƙa rayuwa da tabbatar da cewa gwamnati na tsayawa kan alkawuran da ta ɗauka.

Kwankwaso ya yabi mulkin Abba a Kano

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yaba da ƙoƙarin da daliban jihar su ka nuna a jarrabawar NECO.

Kara karanta wannan

Babu karbo bashi: Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta yi ruwan ayyukan raya Kaduna

Ya ce wannan nasara ba ta tabbata ba sai da ya ga yadda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ba ilimi muhimmanci a jihar fiye da zamanin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

A sakamakon da hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa ta fitar, ya nuna cewa daliban jihar Kano ne su ka yi zarra a tsakanin takwarorinsu a bana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng