'Yan Kasuwa Musulmi na Fuskantar Cin Zarafi, Ana Ƙwace Dukiyarsu da Sunan Sarkin Osun
- ’Yan kasuwa Musulmi a Ile-Ife sun zargi wasu wakilan fada da kwace kayansu saboda kin biyan kudaden bukukuwan gargajiya
- Kungiyar APTAN ta ce wannan zalunci ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya, ta kuma roki Ooni na Ife da ya shiga tsakani
- Kungiyar ta bukaci a daina cin zarafin 'yan kasuwa Musulmi, a mayar da kayayyakinsu, domin mutunta addini da kuma 'yansu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - ’Yan kasuwa Musulmi a masarautar Ile-Ife, jihar Osun, sun roki Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, da ya kai masu daukin gaggawa.
'Yan kasuwar sun ce wasu mutane da suka ce wakilan fadar sarkin ne suna cin zarafi da kwace musu kaya saboda kin biyan kudin bikin gargajiya na Olojo.

Source: Facebook
Kungiyar APTAN, reshen Ile-Ife, ta ce wannan danyen aiki ya sabawa ’yancin addini da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ke faruwa da 'yan kasuwa Musulmi
Sanarwar kungiyar na dauke ne da sa hannun Adegoke Saidi (shugaba), Monsur Jimoh (sakatare), da Banjo Isiaq (Jami’in jin dadin mambobi).
A sanarwar da aka fitar, kungiyar ta ce an kwace kayayyakin 'yan kasuwa Musulmin ne a ranar 16 ga Satumba, 2025, a kasuwar mako-mako ta Ojatuntun Otisese.
Kungiyar ta ce wasu mutane uku, Efunwole Kola, Sogo Olagbaju da Hezekiah Agunbiade ne suka kai samame a kasuwar suka kwashe kayan sawa da man gyada na sayarwa.
Korafin ’yan kasuwa Musulmi na Osun
Sanarwar ta ce:
“Ana kai wa Mambobinmu hari akai-akai, inda ake kwace musu kaya saboda kawai sun ki karya akidarsu.
“Mu ba ’yan tawaye ba ne, mu masu bada gudummawa ne wajen ci gaban Ile-Ife.”
Kungiyar APTAN ta ce tilasta Musulmi biyan kudin bukukuwan gargajiya ya sabawa ka’idojin Musulunci da tsarin mulkin Najeriya.
Shugabannin kungiyar sun kuma yi nuni da ayoyin Suratul Al-An’am 6:162 da Suratul Al-Ma’ida 5:2 da ke cikin AlKur'ani a matsayin hujja.

Source: Original
Abin da 'yan kasuwa Musulmi ke bukata
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Wannan cin zarafi na shekara-shekara haramun ne a Musulunci kuma kalubalantar darajar dimokuradiyyar Najeriya ne.
"Bukatunmu ba su da yawa: a daina cin zarafinmu, a mayar da kayayyakin da aka kwace, kuma a mutunta ’yancinmu na yin addini ba tare da tilasci ba.”
Sun kuma zargi wasu jami’an fada; Babaloja na Odo-Ogbe, Chief Jimoh Olaoluwa Odeyemi, da jagorantar wannan cin zarafi, sai dai sun ce wata kila Ooni na Ife bai san abin da ke wakana ba.
“Muna girmama Mai Martaba Ooni matuka, kuma muna da yakinin cewa idan aka sanar da shi cikakke, zai dauki mataki don kare martabar sarauta da kawo karshen wannan zalunci.
- Adegoke Saidi, shugaban APTAN.
Ooni na Ife ya nada sarakuna 20
A wani labari, mun ruwaito cewa, Ooni na Ile-Ife, Oba Ogunwusi, ya nada sababbin sarakuna 20 a jihar Osun, domi kara hidima ga jama’a.
Daga cikin wadanda aka nada akwai Obajio na Moore, Olu na Erinle da Olu na Ifeparapo, Adetoro na Awoyaya da Olu na Abeji.
An bukaci sababbin sarakunan da su yi mulki da hikima da tawali’u, su kuma raya al’adu da ci gaban tattalin arzikin al’ummominsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


