Ba Ta da Lasisi: An Gano Boyayyen Lamari Game da Jami'ar da Ta ba Rarara Digiri
- Fitaccen Dauda Kahutu Rarara, ya samu digirin girmamawa daga jami’ar European-American, abin da ya haddasa ce-ce-ku-ce
- Legit Hausa ta gano cewa jami’ar E-AU ba ta da lasisi a Amurka ko Birtaniya, kuma babu hukumar da ta amince da sahihancinta
- Shafin jami’ar ya bayyana cewa ba ta da malamai ko ma’aikata kai tsaye, kuma ba ta da wani tsayayyen wurin karatu a Faransa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Ana ta hayya hayya game da digirin girmamawa da wata jami'ar European-American (E-AU) ta ba fitaccen mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara.
Tun bayan da aka ga Dauda Rarara sanye da rigar 'Dakta' tare da gwamnan Katsina, Dikko Radda a lokacin karramawar, aka fara ce-ce-ku-ce.

Source: UGC
Jami'a ta ba Rarara kambun 'Dakta'
Rabi'u Garba Gaya, mai magana da yawun Rarara ne ya wallafa hotuna a shafinsa na Facebook, inda ya ce yanzu mawakin ya zama cikakken 'Dakta.'

Kara karanta wannan
Lamari ya girma: Jami'ar da aka ce ta karrama Rarara ta raba gardama bayan ce ce ku ce
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ce manyan mutane ne suka halarci taron, yana mai cewa:
"Taron ya samu halartar manyan baki, kamar su shugaban jam'iyyar APC na kasa, Hon. Nantawe Yelwada da gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
"Sauran mahalarta taron sun had ada dan takarar gwamnan Bauchi, Bala Wunti da kwamishinan muhalli na Katsina, Hon. Hamza Sulaiman Faskari, da dan majalisar tarayya, Hon. Abdulmalik Zannah (Maru/Bungudu) da Hon. Sani Dan Lami (Katsina ta Tsakiya)."
- Rabi'u Garba Gaya.
An rahoto Rarara, a wata hira da aka yi da shi, yana cewa, yanzu sai a rika lika masa sunan 'Dakta' yayin da za a kira sunansa, watau Dakta Rarara.
Wacce jami'a ce ta ba Rarara digiri?
Ce-ce-ku-ce mai zafi ya barke a soshiyal midiya kan wannan digiri da aka ba Rarara, inda nan take, Legit Hausa, ta gudanar da bincike game da jami'ar European-American (E-AU) da ta karrama Rarara.
A cewar bayanan da aka wallafa a shafin jami'ar na intanet, ita dai E-AU ta na da matsugunni ne a Paris, da ke Faransa, kuma an samar da ita a 2003 don ba da ilimi ga mutanen da suka manyanta.
Daliban jami'ar kan yi karatu ne a fiye da jami'o'i 20 da jami'ar E-AU take hulda da su, ma'ana, duk inda kake a Afrika, Asia, za ka iya yin karatu, ba tare da ka je Paris ba.

Source: Facebook
Jami'ar E-AU ba ta da lasisi
A shafin jami'ar, bangaren tsare-tsaren gudanarwarta, sashen lasisi, da dokoki, Legit Hausa ta fahimci cewa:
- Jami'ar European-American da ta karramar Rarara ba ta da lasisi a Amurka, kuma babu wata hukumar Amurka, walau ta kasa ko ta jiha da ta tantance matsayin jami'ar.
- Jami'ar European-American ba ta kasar Birtaniya ba ce, kuma ba ta da lasisi ko wata shaidar tantacewa ta KRC ko AoP.
- Ita dai kawai jami'ar kasar waje ce da ta ce tana aiki karkashin sashe na 214 na dokar sabunta Ilimi ta 1988, wacce ke karkashin irin tsarin makarantun da ke a karamin sashe na 10(b) na dokar.
- Ba ta da malamai ko ma'aikata, duk wani wanda ke yi mata aiki to yana yi ne a kashin kansa, ba don ta biya shi ba.
'Ba mu karrama Rarara ba' - EAU
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’ar European-American ta yi martani kan maganganu da ake ta yi bayan rahoton karrama Dauda Kahutu Rarara.
Jami'ar ta fitar da sanarwa tana nesanta kanta daga digirin girmamawa da aka ba mawaki Dauda Kahutu Rarara a Abuja, inda ta ce ba ruwanta da lamarin.
Hukumar makarantar ta ce za ta kai maganar ga hukumomin Najeriya domin a hukunta masu yin irin haka, cewar babu hannunta a ba Rarara digiri.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

