Gwamna Abba Ya Canza Wa Ma'aikata Guda Suna a Jihar Kano
- Gwamnan Kano ya amince da canza sunan Ma'aikatar Mata, Yara da Nakasassu zuwa Ma'aikatar Mata, Yara da Masu Bukata ta musamman
- Kwamishina a Ma'aikatar da aka canza sunan, Hajiya Amina Sani Abdullahi ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a Kano
- Hajiya Amina ta bayyana yadda Gwamna Abba ya damu da masu bikata ta musamman, in da ta ce yana yawan tambayar halin da suke ciki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta canza sunan Ma'aikatar Harkokin Mata, Kananan Yara da Nakasassu.
Gwamnatin ta sauya sunan daga Ma'aikatar Mata, Yara da Nakasassu zuwa Ma'aikatar Mata, Yara da Mutane Masu Bukata ta Musamman.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa Gwamna Abba ne ya amince da canza sunan ma'aikatar domin jawo masu bukata ta musamman a harkokin gwamnati.
An canza sunan ma'aikatar mata a Kano
Kwamishinar Ma'aikatar, Hajiya Amina Sani Abdullahi ce ta tabbatar da canza sunan a wata sanarwa da daraktan sashin hulda da jama'a, Bintu Yakasai ta fitar a Kano.
Ta bayyana cewa Gwamna Abba ya amince da wannan canji ne a taron Majalisar Zartarwa ta Jiha (SEC) na baya-bayan nan da aka yi a gidan gwamnatin Kano.
Hajiya Amina ta ce an canza sunan ma'aikatar ne sakamakon bukatar da aka gabatar na a sauya kalmar “Nakasassu” da kalmar da ta fi girmamawa wato “Mutanen Masu Bukatu ta Musamman.”
Ta bayyana cewa kalmar da aka yi amfani da ita a baya ta tsufa kuma ana kallonta a matsayin wacce ke da wata alamar wariya, yayin da sabon sunan yake nuna mutunci tare da bainwa kowa daraja.
Kwamishinar ta ce:
“Babu wanda aka ce cikakken nakasasshe ne, kowa yana da abin kirki da gudummuwar zai iya bayarwa.”
Kwamishinar Kano ta yabi Gwamna Abba
Hajiya Amina ta kuma yabawa Gwamna Abba bisa jajircewarsa wajen kula da mutanen da ke da bukatu na musamman, tana mai cewa goyon bayan da yake ba su na kara masu kwarin gwiwa.
"A duk lokacin da na hadu da mai girma gwamna sai ya tambaye ni ya masu bukata ta musamman suke ciki kuma taya za mu taimaka masu, duk idan muka hadu sai ya mani wannan tambayar," In ji ta.

Source: Facebook
Kwamishinar ta kuma jaddada cewa sake wa ma’aikatar suna ba wai alama ce kadai ba, illa farkon gyare-gyare don tabbatar da hada kai, karfafa gwiwa da kuma samar da dama iri daya ga kowa, in ji Daily Post.
Gwamna Abba zai dauki sababbin malamai
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na shirin daukar ma’aikata 4,315 domin kara bunkasa harkokin ilimi.
Ya bayyana cewa wandanda za a dauka aikin, suna daga cikin wadanda ke koyar wa na wucin gadi a wasu makarantun da ke jihar Kano.
Gwamna Abba ya ce wannan matakin na daga cikin tsare-tsaren gwamnatinsa na farfado da martabar ilimi a jihar Kano.
Asali: Legit.ng


