Obasanjo Ya Yi wa Shugabanni Nasiha Mai Ratsa Zuciya kan Mutuwar Dimokuradiyya
- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce dimokuradiyya za ta rushe idan aka ci gaba da tafiyar da ita ba tare da gyara ba
- Ya bayyana haka ne yayin taro game da dimokuradiyya na gidauniyar Goodluck Jonathan da aka yi a Accra, Ghana
- Rahoto ya nuna cewa Obasanjo ya ce tsarin yanzu ya karkata daga asalin ma’anarsa na mulki domin samar da mafita ga jama'a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ghana – Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi gargadi cewa tsarin dimokuradiyya da ake tafiyar da shi a duniya yanzu na cikin hadarin rushewa.
Ya bayyana hakan ne a wurin taron dimokuradiyya da cibiyar Goodluck Jonathan ta shirya a Accra, babban birnin kasar Ghana.

Source: Getty Images
Leadership ta wallafa cewa Obasanjo ya ce tsarin mulkin dimokuradiyya da aka tsara tun farko domin zama mulki na jama’a ya kauce daga asalin ma’anarsa.

Kara karanta wannan
Jonathan ya kada hantar shugabanni, ya fadi abij da ya kamata a yi wa marasa katabus
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce dole ne a sake fasalta dimokuradiyya ta fuskar ma’ana, tsari da kuma yadda ake aiwatar da ita, idan aka yi niyyar kauce wa mutuwarta gaba daya.
Gargadin Olusegun Obasanjo kan dimokuradiyya
Rahoton New Telegraph ya nuna cewa tsohon shugaban ya bayyana cewa dalilin da ke kawo rauni cikin tsarin shi ne yadda ake tafiyar da shi.
Obasanjo ya yi nuni da cewa yadda ake tafiyar da tsarin yanzu shi ne ke haifar da matsalar da ke sa ya kasa kawo cigaba da daidaito.
A cewarsa:
“Idan ba a yi wa dimokradiyya gyara ba, za ta mutu, sannan a birne ta.”
Obasanjo ya bukaci a yi gyara a dimokuradiyya
Duk da wannan suka, Obasanjo ya bayyana cewa babu wani tsari na mulki da ya dace ya maye gurbin demokradiyya idan aka bi shi yadda aka tsara tun farko.
Ya ce ya kamata mulki ya kasance na dukkan jama’a, amma abin da ake gani yanzu shi ne mulki yana shafar wasu mutane kadan ne maimakon kowa da kowa.
Ya yi suka ga yadda ake fassara demokradiyya da cewa ita ce “mulkin masu rinjaye,” yana mai cewa hakan na ware kananan kabilu daga tsarin.
Obasanjo ya yi tambaya da cewa, idan an ce demokradiyya mulkin masu rinjaye ce, ya za a yi da sauran tsirarun jama'a da ke cikin al'umma?

Source: Twitter
Cif Obasanja ya jaddada batun gyara
Rahotanni sun nuna cewa Obasanjo ya kara jaddada cewa gyara ya zama wajibi domin kare tsarin daga mutuwa.
Ya ce ba za a iya cimma adalci, cigaban kasa da zaman lafiya ba sai an tabbatar da cewa dukkan bangarorin jama’a suna da wakilci da kuma rawar da za su taka.
Kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da ake kara samun damuwa a duniya kan yadda ra’ayin mulkin dimokraɗiyya ke raguwa, tare da karuwar mulkin danniya da raunin hukumomi.
Peter Obi ya gana da Olusegun Obasanjo
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya gana da Olusegun Obasanjo.
Duk da cewa ba a samu cikakken bayani kan abubuwan da suka tattauna ba, wani rahoto ya nuna cewa sun tattauna ne kan batutuwan da suka shafi Najeriya.

Kara karanta wannan
Ribas: Peter Obi ya zargi gwamnatin Najeriya da yi wa dimokuradiyya kisan mummuke
Ganawar na zuwa ne yayin da Peter Obi ke ziyartar shugabanni da manyan kasa, wanda ake ganin hakan na da alaka da gyara tafiyar siyasar shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
