"Da Ya Kai N11m": Yadda NAHCON Ta Nemawa Alhazai Saukin Kudin Hajjin 2025

"Da Ya Kai N11m": Yadda NAHCON Ta Nemawa Alhazai Saukin Kudin Hajjin 2025

  • Shugaban hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON), ya bayyana kokarin da ya yi wajen aikin Hajjin shekarar 2025
  • Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana cewa ya yi kokari wajen ganin Alhazai sun samu rangwame wajen kudin da su ke kashewa
  • Shugaban na NAHCON ya bayyana cewa da ba don kokarin da ya yi ba, da alhazai sun kashe kudade masu yawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yi magana kan sauye-sauyen da ya kawo.

Shugaban na NAHCON ya bayyana cewa ya yi kokari sosai wajen rage kudaden da Alhazai ke kashewa.

Shugaban NAHCON ya yi bayanai kan ayyukan hukumar
Shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman Hoto: @nigeriahajjcom
Source: Twitter

Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NAHCON ta nemawa Alhazai rangwame

Shugaban na NAHCON ya bayyana cewa jin dadin Alhazai shi ne abin da ya sanya a gaba, tun bayan fara jan ragamar hukumar.

Kara karanta wannan

Wike ya tsallake rijiya, ya fadi yadda Janar na soja ya ba da umarnin harbe shi

"Da na hau karagar mulki, abu na farko da na kalla shi ne manufar hukumar. Ainihin manufarta ita ce kula da jin daɗin alhazai, don haka na fara tsara dabaru domin tabbatar da cewa an kula da su yadda ya kamata.”
"Mun fara ne da tuntuɓar masu samar da abubuwa don samun rangwame a kan dukkan kuɗaɗen da suka shafi gudanar da aikin Hajji. Da ikon Allah, mun samu nasarar samun ragi."
"Wataƙila, da ba mu yi haka ba, aikin Hajjin zai iya kai wa fiye da Naira miliyan 11, amma mun samu ragi."
"Misali, kafin na hau kujerar shugabanci, ana cajin kusan Riyal 4,770 a Mina, Arafat da Muzdalifah. Da wannan tsari, na samu an rage Riyal 720 ga kowanne mahajjaci, wanda wannan adadi ne mai yawa."
“Haka kuma, mun samu rangwamen Riyal 200 a kan kowane ayyukan da ake yi wa alhazan Najeriya a Madinah. Idan aka mayar da shi zuwa Naira, kuɗi ne masu yawa."
"Mun kuma samu ƙarin rangwamen Riyal 303 a kan kuɗin sufuri daga Makkah zuwa Mina.”

Farfesan ya kuma bayyana taimakon da suka samu a bara daga gwamnatin tarayya.

"A ƙarshe, domin cika alhakinmu na kula da jin daɗin alhazai, mun nemi goyon bayan gwamnatin tarayya kan batun lafiya, wanda ya kasance babban nauyi ga alhazai."

Kara karanta wannan

Daga Kaduna, Taraba da wasu jihohi ake kai hari a Filato inji rahoton gwamnati

"Gwamnati ta amsa ta kuma kawo kayan magani da darajarsu ta kai ɗaruruwan miliyoyi a lokacin aikin Hajjin. Ba mu taɓa kashe kuɗin hukumar NAHCON a kan waɗannan kayan ba."

- Farfesa Abdullahi Saleh Usman

NAHCON ta nemawa Alhazan Najeriya sauki
Hoton wasu Alhazan Najeriya a kasa mai tsarki Hoto: @nigeriahajjcom
Source: Twitter

Batun binciken EFCC kan ma'aikatan NAHCON

Dangane da binciken da EFCC ke yi kan wasu ma'aikatan hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman ya bayyana cewa ana da ikon yin hakan.

“Wannan hukuma hukumar gwamnati ce, kuma hakkin hukumomin bincike ne su duba duk wani zargi a duk inda ya taso. Babu wanda zai iya tambayar manufarsu ta gudanar da bincike."
"Bayan mun kammala aikin Hajjin da ya gabata, duniya ta amince da shi a matsayin mafi kyawu tun bayan kafuwar hukumar. Ba wani Alhaji guda da ya yi ƙorafi."

- Farfesa Abdullahi Saleh Usman

NAHCON ta fara shirin Hajjin 2026

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta fara shirin aikin Hajjin shekarar 2026.

Hukumar NAHCON ta gudanar da taro da shugabannin hukumomin jindadin Alhazai na jihohin Najeriya.

A yayin taron, shugaban NAHCON ya ce an amince maniyyata su fara ajiye N8.5m domin aikin Hajjin 2026, wanda zai iya sauyawa bayan kammala tattaunawa da masu ruwa da tsarki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng