'Za Mu Dora daga Inda Ya Tsaya,' Anji abin da Tinubu Ya Fadawa Iyalan Buhari a Kaduna

'Za Mu Dora daga Inda Ya Tsaya,' Anji abin da Tinubu Ya Fadawa Iyalan Buhari a Kaduna

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya kai ziyarar ta’aziyya gidan marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a Kaduna a ranar Juma'a
  • Shugaba Tinubu ya karfafi gwiwar iyalan marigayin, yana mai cewa, dukkanin Najeriya tana alhinin rashin Muhammadu Buhari
  • A yayin da Aisha ta yi godiya ga Shugaba Tinubu bisa wannan ziyara, ta roki shugaban kasar ya dora daga inda Buhari ya bari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - A ranar Juma'a, Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyarar ta’aziyya gidan marigayi shugaba Muhammadu Buhari a Kaduna.

Matar Buhari, Aisha, ɗansa Yusuf, da kuma ‘yan uwa da abokan marigayi Shugaba Buhari ne suka tarbi Tinubu.

Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci iyalan marigayi Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi ga Aisha a lokacin da ya kai ziyara ga iyalan Buhari a Kaduna. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Abin da Tinubu ya fadawa iyalan Buhari

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da abin da aka tattauna a ziyarar a sanarwar da ya fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun ankarar da Shugaba Tinubu kan gwamnonin da zai yi hattara da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya rahoto cewa, Tinubu ya shaida wa iyalan Buhari cewa ba su kadai ba ne cikin bakin cikin rashin tsohon shugaban, ya ce Najeriya gaba ɗaya tana cikin alhini.

Shugaba Tinubu, ya fadawa su Aisha cewa:

“Mutuwar mutum ba ita ce take nufin cewa mun rasa shi baki ɗaya ba. Tabbas kyawawan dabi’unsa za su ci gaba da kasancewa tare da mu.
"Ina mai baki da daukacin iyalansa Buhari cewa za mu dora daga inda jagoranmu ya tsaya, za mu ci gaba da bin tafarkinsa na riko da gaskiya, amana, nagarta da kuma kyawawan dabi'unsa.
"Muna rokon Ubangiji ya albarkaci Najeriya, ya ci gaba da hada kanmu a waje daya, daga nan har zuwa tudun mun tsira."

Abin da Aisha Buhari ta fadawa Tinubu

Aisha Buhari, cikin raunannar murya ta nuna jin daɗinta da wannan ziyara, tana mai cewa ta zama babbar tausasa zuciya ga iyalan, yayin da suke makokin rashin Buhari.

Kara karanta wannan

El Rufai ya gargadi 'yan Najeriya kan Tinubu, ya yi hasashen shirinsa kan mulki

"Ina so in yi amfani da wannan damar, in sake yi maka godiya, in kuma godewa uwar gidan shugaban kasa, uwar gidan mataimakin shugaban kasa, bisa kasancewa tare da ni da iyalina a mawuyacin halin da muka shiga," inji Aisha.

Aisha, ta kuma tuna da cewa marigayi Muhammadu Buhari ya tsaya tsayin daka kan gaskiya, amana, da adalci, inda ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi koyi da rayuwarsa.

"Ina rokon Ubangiji ya wanzar da zaman lafiya a Najeriya, ya hada kan kasar, kai kuma, Shugaba Tinubu, ka dora daga inda mijina ya tsaya, ka yi koyi da kyawawan dabi'unsa na rikon gaskiya, amana, hakuri, tausayi da adalci."

- Aisha Buhari.

Shugaba Bola Tinubu da iyalan Buhari sun yi addu'a ga marigayin da Najeriya baki daya.
Shugaba Bola Tinubu da tawagar gwamnoni, ministoci sun kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Buhari. Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

Tawagar da ta raka Tinubu gidan Buhari

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas sun kasance cikin tawagar da ta raka shugaban ƙasa a wannan ziyara.

Haka kuma gwamnonin jihohin Kwara, Yobe, Borno da Sokoto sun halarci wannan ziyara domin kara karfafa iyalan Buhari.

Akwai kuma ministan kuɗi, Wale Edun, ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya samu gagarumin tagomashi yayin da ake tunkarar zaben 2027

Wannan ya nuna irin muhimmancin da gwamnatin Tinubu ta ba ziyarar, wacce ta ƙara kwarin gwiwa ga iyalan marigayi Buhari.

Abin da 'yan Najeriya suka ce kan ziyarar

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu 'yan Najeriya kan wannan ziyarar da kuma maganganun da Tinubu da Aisha suka tattauna:

Aisha Khalid ta bayyana cewa:

"Ai kuwa gaskiya mun ga ya ci gaba daga inda Buhari ya tsaya. Ba wani sauyi da muka gani, talaka dai ke shan wuya. Ba a rabu da Bukar ba an samu Abubakar.

"Amma, ta fuska daya zan yaba masa, abinci ya fara yin sauki gaskiya. To mu dai muna rokonsa a sake kawo hanyoyin da talaka zai samu saukin rayuwa."

Shi kuwa Al'Amin Mohammed Rigasa, cewa ya yi:

"Allah ya jikan Shugaba Muhammadu Buhari, lallai muna kewarsa. Muna addu'ar Allah ya jikansa, su kuma masu 'yan gunaguni su yi ta yi, shi dai ya yi tasa ya gama.

"Maganar kuma Tinubu ya ci gaba daga inda Buhari ya tsaya, ina goyon bayan hakan, don Buhari ne ya dora kasarnan a saiti, kowa ya shiga taitayinsa, talaka ya san ciwon zafin nema, mai kudi ma ya koma tattali."

Kara karanta wannan

Tinubu, 'yan siyasa, malaman Izala da Darika sun cika Kaduna auren dan Sanata Yari

Al'Amin ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ci gaba da yiwa Shugaba Tinubu addu'a, ya sauke nauyin da ke kansa, a cewarsa, Tinubu yana yin abin da ya dace.

Iyalan Buhari sun bar gidansa na Daura

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hajiya Aisha Buhari da ’ya’yanta sun koma Kaduna daga Daura bayan kwanaki da birne tsohon shugaba Muhammadu Buhari.

Mataimakiyar gwamnan Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe ce ta jagoranci tawagar tarbar iyalan Buhari a sansanin sojojin sama da ke jihar.

Bayan tarbar ne kuma aka raka su zuwa gidan da za su ci gaba da zama, wanda yake a Unguwan Rimi GRA, cikin girmamawa da mutuntawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com