Sakkwato: Shugabannin Makarantun Sakandare 6 Sun Tsunduma kansu a Matsala

Sakkwato: Shugabannin Makarantun Sakandare 6 Sun Tsunduma kansu a Matsala

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta dakatar da shugabannin makarantu shida bayan a kama su da laifin da ya saba dokar gudanarwar makarantunsu
  • Tuni gwamnati ta kafa kwamiti mai mutum biyar don bincikar zargin da ake yi musu, yayin da ta ba su umarnin mika ragamar aiki a cikin gaggawa
  • Shugabanninsu sun hada da Nana Girls Secondary School, Government Day Secondary School (GDSS), Gagi da GDSS, Mana

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Gwamnatin jihar Sakkwato ta dakatar da wasu shugabannin makarantu guda shida bisa zargin karɓar kuɗi daga hannun ɗalibai.

Ana zargin shugabannin da umartar daliban da su karbo kudi daga hannun iyayensu ba tare da izini ba, sannan ana zarginsu da kin bin doka a gudanar da aiki.

Kara karanta wannan

Filato: Bincike ya bankado yadda aka hallaka mutum kusan 12,000 a 'yan shekarun nan

An dakatar da Shugabannin Makarantu a Sakkwato
Hoton Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu Hoto: Ahmed Aliyu 2023
Source: Twitter

Channels TV ta wallafa cewa Kwamishinan ilimi a matakin farko da na Sakandare, Farfesa Ahmad Ala, ne ya bayyana haka a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Sakkwato na zargin malamai da laifi

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa a cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Ibrahim Iya, ya fitar, ya ce ana zargin Shugabannin da aikata laifi.

Farfesa Ala ya ce:

“Ba za a bar wani shugaban makaranta ko jami’in gudanarwa ya yi aiki yadda ya ga dama ba, ko kuma ya ci zarafin ɗalibai da iyayensu ta hanyar karɓar kuɗi ba bisa ka’ida ba.”

Ya kara da cewa:

“Dole na makarantu a jihar Sakkwao su kasance a karkashin doka, ba wai ana tafiyar da su don bukatar kai ba.”

Za a binciki Shugabannin makarantu a Sakkwato

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani jami’i da aka samu da laifi.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa 4 da za su koma bakin aiki bayan janye dokar ta baci a Rivers

Ya bayyana cewa an ce an riga an kafa kwamitin binciken mutum biyar karkashin Farfesa Mustapha Tukur domin bin kadun batun.

Wasu daga cikin makarantun da aka dakatar da shugabanninsu sun hada da Nana Girls Secondary School, Government Day Secondary School (GDSS), Gagi da GDSS, Mana.

Sauran makarantun sun hada da Giginya Memorial College, Mana Basic Secondary School da kuma GDSS, Silame.

Ana binciken shugabannin makarantu a Sakkwato
Taswirar jihar Sakkwato, inda aka dakatar da Shugabannin makarantu Hoto: Legit.ng
Source: Original

An bayyana cewa an dakatar da shugaban GDSS, Silame, ne musamman saboda rashin biyayya ga hukuncin gwamnati.

Ma’aikatar ta umarci duka shugabannin da aka dakatar da su mika ragamar gudanar da makaranta ga mataimakan shugabanni masu kula da harkokin gudanarwa cikin gaggawa

Gwamnatin jihar Sakwato ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da da’a, gaskiya da adalci a dukkan makarantun gwamnati na jihar.

An yi hatsarin jirgi a Sakkwato

A baya, mun wallafa cewa wani mummunan hatsarin jirgin ruwa ya afku a jihar Sakkwato ya rutsa da bayin Allah da ke gudun neman tsira da rai daga harin 'yan bindiga.

Rahotanni sun ce jirgin ya nutse ne a ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025, bayan da ya bugi wani bangare na gada yayin da yake tafiya cikin sauri domin gujdewa 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya

An ce jirgin ya cika da fasinjoji, mafi yawancinsu mata da yara da suka tsere daga harin da 'yan bindiga suka kai wa kauyensu, kuma suna kokarin tsallakawa zuwa wani wurin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng